CBN ya janye haramcin amfani da kuɗaɗen Kiripto

0
93

Babban Bankin Najeriya ya janye haramcin da ya sanya kan amfani da kuɗaɗen Kiripto a Najeriya.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito a wata sanarwa daga Daraktan Kuɗaɗe na (CBN), Haruna Mustapha, cewa an janye haramcin kan kuɗaɗen kiripto.

Shekaru biyu kenen bayan haramcin da CBN ya sanya wa kuɗaɗen na kiripto a watan Fabrairun shekarar 2021.

Mustapha ya bayyana cewa nan gaba CBN zai fito da ka’idoji da dokokin amfani da kuɗaɗen na kiripto domin hana wuce gona da iri wajen amfani da su a Najeriya.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta yankewa shugaban Kiripto hukuncin ɗaurin shekaru 11 a gidan yari

A watan Fabrairun 2021 ne CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin hadahadar kuɗaɗe amfani da kuɗaɗen Kiripto ko buɗe wa masu su amfani da su asusun ajiya.

A wancan lokacin, Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya sanar cewa daukar matankin na da muhimmanci domin dakile yiwuwar amfani da kuɗaɗen na kiripto wajen tallafa wa ayyukan ta’addanci.

Bugu da ƙari, kuɗaɗen na kiripto suna tatare da haɗari, sannan babu dokokin da ke kula da su ko na kare kwastomi wajen yin cinikayya da su.

Daraktan na CBN ya ce abubuwan da ke faruwa a duniya suna nuni ga muhimmanci tsara dokokin kula da ƙadarorin intanet irin su kuɗaɗen kiripto da dangoginsu.

Sai dai ya bayyana cewa har yanzu ba a amince wa bankuna da cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe su mallaki kuɗaɗen Kiripto ko su yi kasuwanci da su ta asusun ajiyarsu ba.

Leave a Reply