An Buƙaci Al’ummar Musulmi Su Koma Ga Gwamnatin Allah Don Samun Saukin Rayuwa

0
509

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

AYAYIN da al’ummar Musulmi a fadin duniya ke bikin Sallah Karama na watan Azumin Ramadana, an buƙaci al’umma da mayar da al’amuransu zuwa ga Allah domin samun sauki da mafita daga cikin halin kangi da kuncin rayuwar da suke fuskanta musamman a kasar Najeriya.

Da yake gabatar hudubarsa na Sallar Idin bana a filin Makarantar Sakandaren Gwamnati dake Rigasa Kaduna, Imam Rabi’u Ali Tanko, ya bayyana cewa halin da al’umma suka tsinci kansu a yanzu na rashin tsaro da tsananin rayuwa na da bukatar al’umma su koma ga Allah don neman dauki da samun tsira daga wajen Allah madaukaki.

Limamin ya kara da cewa, babu shakka da akwai bukatar mutane su koma ga Allah musamman a yanzu da al’amarin garkuwa da mutane ya ci karfin al’umma dukda Gwamnati da Jami’an tsaro na iya bakin kokarinsu, toh amma al’amarin na da bukatar yin addu’o’in na neman kariya daga wajen Ubangiji.

Ya ce “mu tuna a rana ta Idin nan, akwai wadansu wadanda yan Uwansu suna can a cikin daji a hannun masu garkuwa da mutane, don haka dole mu taya su da addu’a, sannan su kuma masu yin irin wannan aikin ayi musu addu’ar Allah Ya shiryesu, Ya taba zukatansu, Yasa su gane kimar rayuwar dan Adam don ka da su keta wannan haddin idan suna so su gyara zamantakewarsu tsakaninsu da Ubangiji kuma lahirarsu tayi kyau.

Hakazalika Imam Rabi’u Ali, ya kara da cewa hudubar ta kuma yi bayani a kan zamantakewa tsakanin al’umma wanda ke nuni bisa irin alakar dake tsakani iyalai wanda suka hada tsakanin Ya’ya da iyayensu domin neman Aljannarsu, yanayin zamantakewa tsakanin mata da miji da sauran al’umma domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’umma.

Acewarsa, rashin nuna so da kauna a tsakanin al’umma ne musabbabin duk wata musibar da al’umma ke ciki wacce ta haifar duk wasu tashe-tashen hankali da matsalolin da ake fuskanta, don haka ya zama wajibi al’umma su kaunaci juna, tare da nuna soyayya gaskiya na tsakani da Allah a tsakaninsu domin samun duk wata sauki da mafitar da ake bukata.

Da yake tsokaci kan al’amuran, Sarkin Sabon Garin Rigasa, Kaduna Alhaji Muhammad Jibril, ya bayyana farin ciki bisa samun damar kammala Azumin da a bana aka yi talatin, kana da sake ganin zagayowar wannan rana ta farin ciki da ake bukatar al’umma su nuna farin ciki ta hanyar ziyartar yan Uwansu, kana da yi wa junansu kyakkyawar fata.

Sarkin a matsayinsa na uban kasa na wannan yankin, ya kara da Jan hankalin al’umma musamman matasa da su yi kokarin kiyaye yin duk wasu abubuwan da suka sabawa karantar Addinin Islama domin duk Musulmi ya kamata yasan cewa shi Musulmi ne, kana ya shawarci al’umma da su ci gaba da yin sauran ibadodi kamar yadda Allah Ya ce.

A Karshe, Sarki Muhammad Jibril, ya yi godiya ga Allah bisa ga wannan ni’imar kana da miki gaisuwa ga Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli, Dan Galadiman Zazzau da sauran Sarakuna da daukacin al’ummar Musulmi baki daya musamman na Sabon Garin Gundumar Rigasa.

Leave a Reply