Sallah: Sarakuna A Jihar Kano Sun Bukaci A Ci Gaba Da Yin Addu’ar Samun Zaman Lafiya

0
309

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

MASU Martaba sarakunan Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da na Bichi Alhaji Nasir Ado Bayero da Sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar da na Rano Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa da kuma Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya sun bukaci al’ummar kasar nan da su Kara yiwa Najeriya Addu’o’i na Samun dawamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a kowane lokaci.

Sun yi wannan horon a sakonnin su na barka da Sallah jim kadan bayan kammala Sallah idi da aka gudanar a masarautun su, tare da jaddada cewa yawaita addu’oi zai kawo karshen dukkanin wasu abubuwa dake wakana na tashe-tashen hankula da kuma rashin tsaro.

Haka kuma sarakunan sun yi Kira ga al’ummomin nasu da su ci gaba da yin aiki da abubuwan da suka koya lokaci Azumi wanda hakan zai kyautata zamantakewa da mu’amulla kamar yadda addinin musulunci ya tanada, inda kuma suka yi fatan alheri ga musulmin duniya bisa zagayowar karamar Sallah.

A karshe, sarakunan sun yabawa gwamnatin Jihar Kano saboda kokarin da take yi wajen inganta tsaro da gudanar da aiyukan alheri fadin Jihar kamar yadda ake gani a kowane lungu da sako ba tare da nuna kasala ba.

Leave a Reply