Connect with us

Siyasa

Zaben 2023: Za A Iya Samun Ingantacciyar Sabuwar Najeriya – Dan Takarar Shugaban Kasa

Published

on

Daga; Mustapha Imrana Abdullahi.

BAYAN gudanar da tattaunawa da masu ruwa da tsaki daban – daban a fadin Najeriya baki daya, wani matashi kuma sanannen dan siyasa da ke a kan gaba Mista Gbenga Olawepo – Hashim ya bayyana aniyar neman Jam’iyyar APC ta tsayar da shi takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023 mai zuwa.

Olawepo-Hashim ya kammala shirin sayen fom dinsa domin tsayawa takara a ranar Alhamis mai zuwa a sakatariyar Jam’iyyar APC da ke Abuja, ya jaddada cewa duk da irin halin da kasar take ciki game da batun yanayin tsaro, da kuma irin yadda tattalin arzikin kasa ke cikin wani mawuyacin hali sakamakon rashin matatun mai masu aiki da za su tace albarkatun man da ake da su da kuma rashin wadatacciyar wutar lantarki da rashin samar da wutar da rarraba wa ga masu bukata, duk da hakan za a iya samun Sabuwa kuma ingantacciyar Najeriya.

Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019, ya bayyana cewa “yanayin da harkar siyasa ke ciki a kasa na cikin wani mawuyacin halin, saboda al’amuran kabilanci da yadda wasu ke daukar al’amuran da zafi duk sun mamaye yanayin siyasar da har suke neman kai wa ga samun rikici, kuma hakan na kokarin dakile duk wani shirin samar da kasa dunkulalliya mai al’umma daya.

Ya kara da cewa abu na uku, wadanda suka mamaye harkokin su ne ainihin masu ilimi da suke a cikin jam’iyyu da a koda yaushe suke kokarin samun biyan bukatun kansu musamman a tsawon shekaru Ashirin da hudu bayan an fita daga mulkin soja.

Dan takarar ya ci gaba da bayanin cewa irin kokarin da wasu masu kishin kasa suka yi tun a jamhuriya ta farko ya taimakawa Najeriya ta zamo ta farko a tsakanin kasashen Asiya da Afrika ta fuskar ma’aunin tattalin arzikin kasa da za a bayar da misali da kasashen Malaysiya da Tailan duk tuni an mance da shi, amma duk da haka har yanzu da akwai yadda za a yi a gyara wannan tsarin tattalin arzikin da wasu suka lalata da nufin samar da ginanniyar sabuwar Najeriya mai inganci.

Kamar yadda ya ce, “wannan samar da karfin zai taimaka wajen samar da hasken da zai shafe duhu a kasar mu. Don haka akwai wani babban abin dubawa ga duk mai kishin kasa da nufin magance dukkan wani tsarin da zai kawo wa kasa cikas.”

“Na fito ne domin tabbatar da matsayi na game da zama shugaban tarayyar Najeriya a zaben shekarar 2023 mai zuwa”.

“Ni nawa ba wai buri ba ne kawai sai dai wani al’amari ne da ya kasance na tarihi da ke tare da ni tun a lokacin da ina karatu a jami’a mu na ta fafutuka kamar yadda kowa ya sani wandda a halin yanzu muke kokarin samar da bunkasasshen tattalin arziki a Najeriya, da kuma kokarin samar da ingantaccen tsarin mulkin Dimokuradiyya”.

Ya kara da cewa babu wani abu da zai gagari yan Najeriya daga yanayi da kuma taimako. “Saboda haka na fito ne in samar da shugabanci da zai samar da yanayi mai kyau a kasa”, ya kuma yi alkawarin cewa ya na da tsare – tsaren tattalin arzikin kasa da za su bunkasa Najeriya da za a samu sabuwar Najeriya da ya samar a cikin Kudirori 50 da za a fitar da su ga kowa ya gani nan ba da dadewa ba da ikon Allah.

Hamshakin dan kasuwar na kasa da kasa mai sana’ar Man fetur ya ci gaba da tabbatar da cewa sabuwar Najeriya da za ta iya zama da kanta a ciki da wajen kasar musamman daga duk wata barazana, da za ta samawa matasan ta aikin yi da a halin yanzu suke neman aiki za a samu ingantaccen tattalin arzikin kasa da nufin rage radadin talauci da cin hanci da karbar rashawa duk za a iya cimma wadannan bukatu domin masu yuwuwa ne.

Ya yi alkawarin dinke barakar da take tsakanin Arewa da kudu a Najeriya, domin magance ciwon a dawo da kasar dunkulalliya da ake zaune tare da Juna kamar yadda aka santa a can baya.

“Ni mahaifina ya kasance dan Arewacin Najeriya ne kuma mahaifiya ta yar Kudancin Najeriya ce. Don haka rabi daga cikin dangina Kiristici ne wasu kuma Musulmai ne.

“Na zauna na yi makaranta a bangaren kudu da Arewa haka kuma a yankin tarayyar Turai da Amurka. Don haka na san cewa an halicci dan-Adam duk daya ne don haka suke da yanci daidai, samun dama da yi wa kowa adalci.

” Zan yi wa kowa adalci ba tare da nuna wani bambanci ba game da batun kabilanci, addini ko jinsi na banbanta mace ko Namiji. Wannan fa ba wani alkawari ba ne da ba zan iya cikawa ba kamar yadda wasu yan siyasa kan yi. Hakika ni haka nake”, inji shi.

Tun lokacin da yake kokarin ganin ya kare hakkin jama’a tsawon shekaru Talatin da suka gabata, Olawepo – Hashim, ya yi abubuwa da dama a harkokin kasuwanci sabanin sauran wadansu da suka yi zamansu cikin jin dadi kamar yadda aka saba su na tafiyar da kungiyoyi masu zaman kansu, Kafafen yada labarai da kuma yin aiki a cikin jami’o’i.

A matsayinsa na shugabannin farko a siyasa bayan da sojoji suka kau a shekarar 1999, ya zamo mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyya mai mulki da kuma shugaban gungun mutane 54 na majalisar zartaswar jam’iyyar da su kansa ya kafa.

Ya fita daga cikin jam’iyyar PDP a shekara 2006 bayan da aka samu ja- inja mai yawa a kan al’amuran da suka shafi harkokin Dimokuradiyyar cikin gida na jam’iyya.

Ya yi karatun aikin jarida a matakin digiri daga jami’ar Legas, da kuma karatun digiri na biyu a kan harkokin da suka shafi duniya a jami’ar Buckingham da ke kasar Ingila inda ya zamo dalibin da ya fi kowa kwazo a wannan lokacin abin da ya bashi damar zamowa na farko a cikin jerin daliban da suka yi karatu a wannan lokacin.

Olawepo-Hashim wanda ya kasance ya na cikin shekarunsa na Hansin, ya zama matashi mai jiki a Jika da ke da masaniya a game da harkokin tattalin arziki, harkokin tsaro da dukkan yadda za a inganta lamarin da ya sha yin magana a kansu a tsawon shekaru hudu da suka gabata.

Hakazalika, ya kasance yana da kwarewa sosai a aikace da kuma ta hanyar rubutu ban da kuma yadda yake yin harkar kasuwanci irin na kasa da kasa. Ya kuma yi karatu a sashen harkokin kudi, harkokin tattalin arziki da kuma harkokin tsaro duk a na kasa da kasa baki daya.

Ni ɗan jarida ne mai zaman kansa. Mawallafi kuma mai sharhi a lamarin yau da kullum.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Siyasa

APC ta dakatar da ɗan Majalisa kan cin amana a Zamfara

Published

on

APC ta dakatar da ɗan Majalisa kan cin amana a Zamfara

Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta dakatar da Ɗan Majalisar Wakilai, Aminu Jaji bisa wasu zarge-zargen da ake yi masa na cin amanar jam’iyyar.

Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar APC na Jihar, Malam Yusuf Idris ne ya sanar da dakatarwar a wani taron manema labarai a Gusau a ranar Juma’a.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Jaji yana wakiltar mazaɓar Ƙaura-Namoda/Birnin-Magaji a Majalisar Wakilai a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Idris ya ce wasu zarge-zargen da ake yi wa Ɗan Majalisar sun haɗa da aikata rashin gaskiya da rashin zuwa tarurrukan jam’iyyar da kuma sauran ayyuka.

KU KUMA KARANTA: Kotun Najeriya ta bayar da umarnin dakatar da asusun banki fiye da dubu 1

Ya ce, matakin ya biyo bayan sanarwar dakatarwar da aka yi wa Jaji daga shugabannin jam’iyyar APC na mazaɓar Birnin-Magaji bisa zargin cin amanar jam’iyyar da dai sauran abubuwan da suka saɓa wa jam’iyyar.
Idris ya ce, “Kwamitin zartaswa na jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Birnin Magaji ne ya miƙa sanarwar dakatarwar zuwa hedikwatar jam’iyyar APC ta jihar.

Bayanai sun ce kwamitin zartaswar jam’iyyar APC na jihar ya gudanar da taron gaggawa a sakatariyar jam’iyyar da ke Gusau a ranar Juma’a 17 ga watan Mayu, 2024, inda aka gabatar da batun dakatar da Jaji ga ‘yan majalisar zartarwar jihar.

Continue Reading

Labarai

Tsohon gwamnan Katsina, Shema ya sauya sheƙa zuwa APC

Published

on

Tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shema, a hukumance ya koma jam’iyyar APC Mai mulki a jihar.

Shema, ya kasance gwamnan jihar a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2015, a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

Tsohon gwamnan ya yi rajista ne a ofishin jam’iyyar na mazaɓar Shema, ƙaramar hukumar Dutsin-ma, inda shugaban jam’iyyar na jihar, Sani Aliyu-Daura ya ba shi katin zama ɗan jam’iyyar APC.

Lambar katin Shema ta zama ɗan jam’iyyar ita ce: 26551.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Yobe za ta mayar da kwale-kwalen Dufuna mai shekaru 8,000 zuwa cibiyar yawon buɗe ido

Malam Aliyu-Daura ya yabawa Gwamna Dikko Raɗɗa da kuma tsohon gwamnan jihar Aminu Masari wanda ya gada, a bisa rawar da suka taka wajen ganin Shema ya sauya sheƙa.

Don haka ya tabbatar wa tsohon gwamnan cewa za a yi masa adalci kamar kowane ɗan jam’iyya.

Shugaban ma’aikata na Raɗɗa, Jabiru Abdullahi-Tasuri, shi ne ya miƙa katin zama ɗan jam’iyya ga Shema a madadin gwamnan a jiya Alhamis a Dutsin-ma.

Continue Reading

Labarai

Fusatattun matasa sun lakaɗawa kwamishina duka a wajen zaɓen fidda gwani

Published

on

Banji Ajaka, kwamishinan lafiya na jihar Ondo, ya gamu da fushin matasa a jiya Asabar yayin da ake gudanar da zaɓen fidda gwani na gwamna na jam’iyyar APC mai mulki a jihar.

Daily Trust ta gano cewa Dakta Ajaka, wanda ke Mazaɓar Ugbo 3, a ƙaramar hukumar, ana zarginsa da ɓoye takardar sakamakon zaɓen.

Shaidu sun tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa da suka yi da manema labarai, inda suka yi zargin cewa fusatattaun matasan ‘ya’yan jam’iyyar APC ne da ke adawa da tsarin da aka bi wajen gudanar da zaɓen.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka shaida lamarin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa rikicin ya faro ne lokacin da ‘yan ɗaya ɓangaren na jam’iyyar suka buƙaci ganin takardar sakamakon zaɓen na fidda gwani.

KU KUMA KARANTA:An yi jana’izar tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu

“Sun fusata ne suka buƙaci jami’in zaɓe ya ba su takardar sakamakon zaɓen sai kuwa ya ce ta na wajen Ajaka.

“Don haka suka yi masa duka a wurin, inda kuma garinsu ne. Jama’a sun fusata sosai da lamarin, inda rigimar ta ƙare a wajen.”

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Dakta Ajaka ya ce an zarge shi ne da riƙe takardar sakamakon zaɓen.

Ya yi bayanin cewa a lokacin da yake ƙoƙarin bayyana kansa, ’yan daban sun auka masa inda suka yi masa mugun duka.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like