Ba Za Mu Ci Amanar Kowa Ba – Ibrahim Datti

0
437

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

DAN takarar majalisar wakilai ta tarayya karkashin Jam’iyyar NNPP, Honarabul Ibrahim Datti da ake yi wa lakabi da “kwamanda”, ya bayyana cewa babban abin da zai mayar da hankali a kansa idan an zabe shi dan majalisar wakilai ta kasa shi ne rikon gaskiya da Amana.

Ibrahim Datti da wasu ke kiransa da Yaron kirki ya bayyana hakan ne a wajen taron murnar bikin Sallah da aka tara yayan jam’iyyar NNPP a Jihar Kaduna.

Datti ya ci gaba da cewa idan an zabe shi zai tabbatar da rikon gaskiya da Amana a tsakanin al’umma saboda haka idan aka ba shi amanarsu ba zai yi kasa a Gwiwa ba.

Matasa maza da mata sun halarci wannan taron inda suka yi jawabin bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga tafiyar Datti Kwamanda Yaron kirki, Inda suk bayyana cewa tafiya ce ta neman tsira, mutunci, martaba da samun natsuwa da ci gaban da kowa ke bukata.

Abba Umar Paki mazabar Unguwar Sanusi na daga cikin wadanda suka halarci babban taron walimar yayan Jam’iyyar NNPP da Honarabul Ibrahim Datti yaron kirki ya kira da aka yi a Kaduna.

Leave a Reply