Connect with us

Siyasa

Buri Na Samar Da Zaman Lafiya A Jihar Kaduna – Abdulmalik Durunguwa

Published

on

Daga; Mustapha Imrana Abdullahi.

DAN takarar Gwamnan Jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar APC Dokta Muhammad Abdulmalik Durunguwa, ya bayyana cewa burinsa shi ne samar da dauwamammen zaman lafiya a Jihar Kaduna.

Abdulmalik Durunguwa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen bude bakin da ya shiryawa yan jarida da aka yi a cibiyar yan jarida ta kasa reshen Jihar Kaduna.

Durunguwa ya ce akwai wani abu da wasu ba su sani ba shi ne ko shugabanni kansu su na matukar jin tsaro a yanayin rashin tsaro.

“Don haka babban buri na shi ne in samar da tsaron lafiya da dukiyar al’umma idan Allah ya ba ni mulkin Jihar Kaduna”.

“Duk a cikin yan siyasar da ke neman wannan shugabancin Jihar Kaduna babu wanda ya fi ni sanin ciki da wajen Jihar, domin babu wani sako da lungun da ban Sani ba a Jihar”, inji Durunguwa.

“Ina yin siyasa tun a shekarar 1982 zamanin siyasar Shagari muna cikin jam’iyyar NPN don haka ina da masaniyar siyasa sosai fiye da sanin wadansu mutane”.

“Kuma wani lamarin da zan tabbatar idan na zama Gwamnan Jihar Kaduna shi ne tare da al’umma za a samar da ingantaccen tsarin tsaro da zai amfani kowa”.

Hakazalika “idan yankunan karkara sun samu ingantattun asibiti, wadatacciyar wutar lantarki, hanyoyi masu kyau da ingantar harkar Noma babu wanda zai zo cikin Birni har ya kai ga zama a wurin kowa zai zauna a inda yake domin ya samu komai a wadace”. kamar yadda Durunguwa ya tabbatar.

Saboda ni buri na shi ne samar da ingantacciyar Jihar Kaduna da kowa zai ji dadin ta a koda yaushe, domin haka da zarar na samu mulki a shirye nake in yi aikin da kowa zai ce Allah sam barka sakamakon farin cikin da mutane suka samu kansu a ciki.

Sai dai Abdulmalik Durunguwa ya yi kira ga manema labarai da su bayar da rahoton kowa ne dan takara da yazo ko ya nemi su isar da sakonsa ga jama’a.

Ya kuma ce ” hakika yankunan karkara na matukar bukatar a kula da su ta fuskar aiki da sauran abubuwan more rayuwa, ni na fito daga kauyen Ladduga ne a karamar hukumar Kachiya, kuma ina alfahari da hakan”.

Abdulmalik Durunguwa wanda kwamishina na Gwamnatin tarayya a hukumar Kidayar jama’a ta kasa mai kula da shiyya, ya fadakar da daukacin al’umma game da bukatar da ke akwai na kula wa da yawan jama’a domin samun damar daukar nauyinsu.

“Saboda duk shugaban da bai kula da wannan tsarin na yawan jama’a ba, to zai zamo kawai ana dai yi ne kawai kamar abin da ake cewa ana tukkar gaba baya na warwarewa wanda hakan ba alkhairi ba ne ta fuskar ci gaban kasa, mutane su dawo daga irin tunanin nan na in auri mace kawai ta ci gaba da haihuwa ba tare da tunanin yadda za a rike yayan ba, domin ni na sha Gwagwarmayar rayuwa fiye da tunanin jama’a don har yaron mota na yi da dai sauran fadi tashi da damar gaske har inda Allah ya kai ni a yanzu”, inji Duringuwa.

Sai ya yi kira ga jama’a da su rika sawa a ransu cewa da ikon Allah duk abin da suke tunani a duniya mai yuwuwa ne.

Ya ce dalibansa da ya koyawa darasin  lisaafi a matakin makarantar Sakandare duk a yanzu sun shigo cikin wannan yunkurin nasa na zama Gwamnan Jihar Kaduna domin wasu a cikinsu manajoji ne a wuraren ayyuka daban daban wasu kuma sun samu matsayi babba a wuraren da suke yin aiki, kana ya kara da tabbatar da cewa idan Ɗaliban da ya Koyar da su ilimin lissafi za su iya kaiwa a halin yanzu wuraren da suke, wannan abin farin ciki ne kwarai a gare shi da sauran al’ummar Jihar Kaduna.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Siyasa

APC ta dakatar da ɗan Majalisa kan cin amana a Zamfara

Published

on

APC ta dakatar da ɗan Majalisa kan cin amana a Zamfara

Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta dakatar da Ɗan Majalisar Wakilai, Aminu Jaji bisa wasu zarge-zargen da ake yi masa na cin amanar jam’iyyar.

Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar APC na Jihar, Malam Yusuf Idris ne ya sanar da dakatarwar a wani taron manema labarai a Gusau a ranar Juma’a.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Jaji yana wakiltar mazaɓar Ƙaura-Namoda/Birnin-Magaji a Majalisar Wakilai a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Idris ya ce wasu zarge-zargen da ake yi wa Ɗan Majalisar sun haɗa da aikata rashin gaskiya da rashin zuwa tarurrukan jam’iyyar da kuma sauran ayyuka.

KU KUMA KARANTA: Kotun Najeriya ta bayar da umarnin dakatar da asusun banki fiye da dubu 1

Ya ce, matakin ya biyo bayan sanarwar dakatarwar da aka yi wa Jaji daga shugabannin jam’iyyar APC na mazaɓar Birnin-Magaji bisa zargin cin amanar jam’iyyar da dai sauran abubuwan da suka saɓa wa jam’iyyar.
Idris ya ce, “Kwamitin zartaswa na jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Birnin Magaji ne ya miƙa sanarwar dakatarwar zuwa hedikwatar jam’iyyar APC ta jihar.

Bayanai sun ce kwamitin zartaswar jam’iyyar APC na jihar ya gudanar da taron gaggawa a sakatariyar jam’iyyar da ke Gusau a ranar Juma’a 17 ga watan Mayu, 2024, inda aka gabatar da batun dakatar da Jaji ga ‘yan majalisar zartarwar jihar.

Continue Reading

Labarai

Tsohon gwamnan Katsina, Shema ya sauya sheƙa zuwa APC

Published

on

Tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shema, a hukumance ya koma jam’iyyar APC Mai mulki a jihar.

Shema, ya kasance gwamnan jihar a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2015, a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

Tsohon gwamnan ya yi rajista ne a ofishin jam’iyyar na mazaɓar Shema, ƙaramar hukumar Dutsin-ma, inda shugaban jam’iyyar na jihar, Sani Aliyu-Daura ya ba shi katin zama ɗan jam’iyyar APC.

Lambar katin Shema ta zama ɗan jam’iyyar ita ce: 26551.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Yobe za ta mayar da kwale-kwalen Dufuna mai shekaru 8,000 zuwa cibiyar yawon buɗe ido

Malam Aliyu-Daura ya yabawa Gwamna Dikko Raɗɗa da kuma tsohon gwamnan jihar Aminu Masari wanda ya gada, a bisa rawar da suka taka wajen ganin Shema ya sauya sheƙa.

Don haka ya tabbatar wa tsohon gwamnan cewa za a yi masa adalci kamar kowane ɗan jam’iyya.

Shugaban ma’aikata na Raɗɗa, Jabiru Abdullahi-Tasuri, shi ne ya miƙa katin zama ɗan jam’iyya ga Shema a madadin gwamnan a jiya Alhamis a Dutsin-ma.

Continue Reading

Labarai

Fusatattun matasa sun lakaɗawa kwamishina duka a wajen zaɓen fidda gwani

Published

on

Banji Ajaka, kwamishinan lafiya na jihar Ondo, ya gamu da fushin matasa a jiya Asabar yayin da ake gudanar da zaɓen fidda gwani na gwamna na jam’iyyar APC mai mulki a jihar.

Daily Trust ta gano cewa Dakta Ajaka, wanda ke Mazaɓar Ugbo 3, a ƙaramar hukumar, ana zarginsa da ɓoye takardar sakamakon zaɓen.

Shaidu sun tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa da suka yi da manema labarai, inda suka yi zargin cewa fusatattaun matasan ‘ya’yan jam’iyyar APC ne da ke adawa da tsarin da aka bi wajen gudanar da zaɓen.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka shaida lamarin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa rikicin ya faro ne lokacin da ‘yan ɗaya ɓangaren na jam’iyyar suka buƙaci ganin takardar sakamakon zaɓen na fidda gwani.

KU KUMA KARANTA:An yi jana’izar tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu

“Sun fusata ne suka buƙaci jami’in zaɓe ya ba su takardar sakamakon zaɓen sai kuwa ya ce ta na wajen Ajaka.

“Don haka suka yi masa duka a wurin, inda kuma garinsu ne. Jama’a sun fusata sosai da lamarin, inda rigimar ta ƙare a wajen.”

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Dakta Ajaka ya ce an zarge shi ne da riƙe takardar sakamakon zaɓen.

Ya yi bayanin cewa a lokacin da yake ƙoƙarin bayyana kansa, ’yan daban sun auka masa inda suka yi masa mugun duka.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like