AMDF Ta Horar Da ‘Yan Jaridu 25 A Kan Jagoranci Da Tsarin Dabaru

0
445

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

GIDAUNIYAR ci gaban kafafen yada labarai ta Afrika (AMDF) tare da hadin gwiwar kungiyar ‘yan Jaridu ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Kaduna, sun horas da ‘yan Jaridu 25 bisa fannin Jagoranci da yin tsare-tsare.

Horon wanda ya dauki tsawon kwanaki biyu na da nufin inganta al’amuran yau da kullum na mahalarta taron bisa fannin jagoranci da basirar gudanarwa, kulawa da yin aiki, warware rikice-rikice, jagoranci da horarwa.

Daya daga cikin ma’aikatan da ke rike da mukamin babban Daraktan gidauniyar, Mista Iliya Kure ya bayyana cewa shugabanci shi ne ikon yin tasiri da dabi’u da kuma yadda wasu ke gudanar da ayyukansu domin cimma wata manufa daya.

Ya shawarci mahalarta taron wadanda su ne shugabannin zartarwa na majalisar da kuma shugabannin duk wasu cibiyoyin Kungiya da ke Kaduna da su tabbatar sun kasance da manufa guda wadda magadansu za su gada yayin da suka yi murabus daga ofis.

Kure ya bukace su da su rungumi dabi’ar koyawa da nasiha ga wasu da za su iya gudanar da ayyukansu na gaskiya idan ba su nan.

Ya ce jagoranci shi ne samar da abubuwa guda biyu wadanda yake kwarin gwiwa da sakamako, amma ya kamata mahalarta taron da su zaburar da mambobinsu domin hakan zai taimaka wajen ci gaban dabi’ar samar da manufa mai inganci.

Daya daga cikin mahalarta taron wacce ita ce shugabar kungiyar NUJ ta Kaduna, Asma’u Yawo Halilu ta bukaci ‘yan kungiyar da su yi amfani da ilimin da suka samu na horon wajen tafiyar da al’amuran Kungiyoyin su daban-daban.

“An rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna a makonni biyu da suka wuce, kuma yanzu mun kammala horas da shugabannin, daga bisani kuma ‘yan Kungiyoyi daban-daban za su gudanar da nasu horon.”

Idan dai za a iya tunawa, kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya, NUJ, reshen Jihar Kaduna, ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da gidauniyar ci gaban kafofin yada labarai ta Afrika (AMDF) kan horon jagoranci.

Ana sa ran wa’adin yarjejeniyar zai dore a tsawon wa’adin sabon shugaban amma za a sake duba shi duk shekara domin tabbatar da cikar manufarsa.

Leave a Reply