Akwai Bukatar Dakarun Sojoji Su ‘Yanto Mazaba Ta Daga Hannun Boko Haram – Inji Kakakin Borno

0
252

Daga; Sani Gazas Chinade, Maiduguri.

KAKAKIN majalisar dokokin Jihar Borno Abdulkarim Lawan ya yi kira ga dakarun tsaron kasar nan da su dukufa wajen kokarin sake ‘yan to mazabarsa ta Guzamala tare da Kukawa daga mamayar ‘yan bindigar Boko Haram da ISWAP.

Kakakin majalisar dokokin na Borno ya bayyana hakan ne ya yin bikin rarraba kudaden tallafin karatu kashi na 4 ga wasu daliban mazabarsa ta Guzamala kimanin 446 da ke karatu a manya-manyan makarantun karo ilimi mai zurfi da aka gudanar a Kwalejin Ilimi ta Kashin Ibrahim da ke garin Maiduguri wadda Sarakuna iyayen kasa da sauran manya-manyan ‘yan siyasa suka halarta

Kamar yadda wakilinmu ya ruwaito kakakin majalisar dokokin na Borno ya jaddada cewar, rashin Jami’an soja a wannan mazaba ta su ta Guzamala da kuma kukawa ya sa ‘yan bindigar Boko Haram da ISWAP na cin karen su babu babbaka a wannan Yanki na su wadda kan haka suke rokon rundunar sojan kasar nan da ta sake kai dakarun su wannan yanki na su don kwato su daga mamayar wadannan ‘yan bindiga na Boko Haram.

“Don haka ina amfani da wannan dama wajen kira da roko ga shugaban rundunar sojojin kasar nan Janar Lucky Irabor da ya kawo musu dauki dangane da wannan kokari da suke yi na Yaki da masu tada kayar baya na Boko Haram/ ISWAP da rundunar ‘Operation Hadin Kai’ don ‘yanto wannan yanki namu na Guzamala da kuma yankin Kukawa.”

Kamar yadda kakakin majalisar ya ce “A yanzu haka kusan dukan bangarorin karamar hukumar su ta Guzamala har ya zuwa yanzu na karkashin kulawar kungiyar Boko Haram ne kasancewar babu jam’in tsaro ko da daya a dukan fadin wannan karamar hukuma ta Guzamala hatta a shalkwatar karamar hukumar babu jami’in tsaro ko daya a cikin garin wadannan ‘yan tada kayar baya na Boko Haram suke cin karen su ba babbaka a dukannin yankin na Guzamala.”

Ya ce “a halin da ake ciki kusan babu wani mai ruwa da tsaki na al’ummar mu da ke zaune a wannan yanki tun daga kan Jami’an karamar hukumar, Hakimai da sauran su duka suna Sansanonin ‘yan Hijira da ke garuruwan Nganzai, Monguno da sauran kananan hukumomin makwabta ciki har da babban birnin Jihar Maiduguri na tsawon shekaru 6 da suka shude zuwa yau din nan da mu ke ciki.”

Acewarsa, yanzu haka mutanen mu sun zaku don su koma garuruwan su, amma abin ban takaici wannan ba shi ne karo na farko ba na ke kira ga Jami’an tsaron don kai Jami’an tsaron soja yankin na Guzamala don al’ummomin mu su samu shiga cikin kokarin da Gwamna Babagana Zulum da ya ke yi na mayar da ‘yan hijirar da jami’an sojoji suka ‘yanta yankunan su ya zuwa garuruwan su na asali. Don haka ina fada da babbar murya cewar, yankin Guzamala na karkashin Boko Haram ne har gobe.”

Abdulkarim Lawan Wanda shi ne kakakin majalisar dokokin wata Jihar mafi dadewa a kasar nan amma duk da haka yana kalubalantar Jami’an sojan kasar nan bisa ga yadda suke gudanar da yaki da ‘yan ta’addar Boko Haram a yankin Arewa mso gabas.

Kakakin majalisar dokokin ya bayyana cewar, wannan tallafin karatu ya bada shi ne ga daliban da suka cancanta musamman wadanda rikicin Boko Haram ya shafa, kuma ya lakabawa wannan tallafin karatu da su na Abdulkarim Lawan scholarship Committee (HALSC) wadda Wakil Sheriff ke jagoranta.

Ya kuma yi kira ga daliban da suka amfana da wannan tallafi da su mayar da hankalin su wajen karatun su, kuma ya ba su tabbacin cigaba da tallafawa harkokin karatun su don ganin sun amfani kan su da ma al’ummomin su.”

Leave a Reply