Connect with us

Labari

Mun Yi Tir Da Tabarbarewar Tsaro; Amma Ba Mu Ce Buhari Ya Sauka Ba – JNI

Published

on

Daga Wakilinmu

Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta yi Allah wadai da tabarbarewar tsaro a Najeriya; amma ta karyata rahotannin da ke cewa ta ce Shugaba Buhari bai cancanci cigaba da shugabancin Najeriya ba.

Da ta ke bayani ta bakin Babban Sakatarenta, Dakta Khalid Aliyu, JNI ta ce abin da ta ce a sanarwarta, wadda shi Dr Khalid ya rattaba wa hannu shi ne ta na mai bayyana rashin jin dadinta saboda radadin yanayin rashin tsaro a kasar ke haddasawa, ta na mai kiran da hukumomi su tashi haikan wajen daukar matakan da su ka dace.

JNI ta ce ta ko ina ka duba yanayin tsaro ya sukurkuce: Kama daga zubar da jinni, zuwa sace sacen mutane sa sauran tashe tashen hankula da ake fama da su a kasar.

Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari

JNI ta ce Allah ya dora ma gwamnatin Najeriya nauyin tabbatar da tsaro a kasar. “Ita gwamnati ta tashi, wannan wajibi, ita Allah ya dora wa. Batun tsaro dai ba wani mutumin da zai iya zuwa ya ce zai tinkari harkar tsaro sai ita gwamnati da yake dama wannan wajibinta ne kuma aikinta ne.

“ Dakta Khalid ya kara da cewa, “Kodayake ta na kokarinta matukar iyawa, to amma dai akwai bukatar ta kara himma; ta kara himma har sai tsaro ya dawo al’umma ta zauna lafiya ana harkoki da tafiye tafiya ba cikin halin dar dar ba; ba a cikin halin barazana ba.”

JNI ta ce a duk duniya, muddun gwamnati ta kasa wajen tabbatar da tsaro to “kasancewarta a matsayin gwamnati akwai damuwa. Wannan shi ne abin da mu ka fada. Babu wani wanda ya kira sunan Shugaban kasa ya ce shi bai kamata ba. Wanda ya ke so ya jefi shugaban kasa da magana to sai ya jefe shi da bakinsa ya ce Shugaban kasa ya tashi ya tafi – wannan kuma ya zama fassararsa kenan – idan abin da yak e son cewa kenan – sai ya je ya rubuta irin na shi. Amma mu dai ba abin da mu ka rubuta ba kenan.”

Da yake amsa tambaya, Dakta Khalid ya ce idan aka ce shugaban kasa ya tafi “to shi kenan sai kasar ta zama babu shugaba kenan? Ai wani rikicin ne kuma zai sake dawowa. Don haka ba wannan bayanin aka yi ba.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labari

EMAS69 • LINK ALTERNATIF SPORTBOOK SBOBET

Published

on

By

Emas69 adalah bandar taruhan sportbook sbobet terlengkap yang saat ini sangat dikenal seluruh masyarakat Indonesia dengan melalui link alternatif Emas69. Pada permainan taruhan sportbook, setiap pertandingan sepak bola yang dilangsungkan dapat dijadikan sebagai tempat bagi seluruh masyarakat Indonesia untuk melakukan taruhan dengan menggunakan uang asli. permainan taruhan bola online dapat dilakukan dengan bebas sesuai dengan pertandingan yang berlangsung dan juga team sepak bola yang disenangi untuk memperoleh kemenangan dan kepuasan dari setiap taruhan sportbook di situs Emas69.

Continue Reading

Labari

Albashi mafi ƙaranci: Da babu gara ba daɗi – TUC/NLC

Published

on

Albashi mafi ƙaranci: Da babu gara ba daɗi - TUC/NLC

Albashi mafi ƙaranci: Da babu gara ba daɗi – TUC/NLC

Shugabannin ƙwadagon sun bayyana matsayar gabanin gabatar da tayin ga majalisun ƙwadagon don gamsar da su amincewa da hakan ya fi a’ala.

Gamayyar ƙungiyar ƙwadagon Najeriya ta ce tayin Naira 70,000 da shugaba Tinubu ya yi a matsayin mafi ƙarancin albashi da babu ne gara ba daɗi.

Shugabannin ƙwadagon sun bayyana matsayar gabanin gabatar da tayin ga majalisun ƙwadagon don gamsar da su amincewa da hakan ya fi a’ala.

KU KUMA KARANTA:NLC ta ƙira taron gaggawa bayan gwamnati ta jingine batun ƙarin albashi

Wannan dai na nuna a karo na farko tun neman mafi ƙarancin albashi mafi yawa a Najeriya Naira 615,00 ya sauƙo Naira 477,000, shugabannin ƙwadagon sun maida wuƙa kube ta hanyar yin na’am da tayin da gwamnati ta yi.

Bayan kammala ganawa babban sakataren ƙungiyar ƙwadagon ta TUC Komared Nuhu Toro ya ce sun amshi tayin da gabatar da hakan gaban majalisun su “mun kai majalisar ƙolinmu, tayin da shugaban ƙasa ya bayar sun kuma lamunta da shi da fatan Allah ya sa albarka…ai Naira 70,000 ɗin nan da babu ne gara ba daɗi.

Tuni ma’aikata na sassa daban-daban suka fara maida martani da mafi sauƙin shi ne na nuna ba abun da suka iya don jagorori sun miƙa wuya.

Malamin makaranta Muhammad Bello Nawaila ya ce ba wani tasiri da mafi ƙarancin albashin zai yi in an duba ɗan karen tsadar rayuwa.

Ita ma ƙungiyar gamayyar ƙungiyoyin arewa CNG da ke marawa gwagwarmayar ma’aikatan baya ta ce matuƙar shugaba Tinubu bai yi garambawul ga lamuran walwalar ma’aikata da matasa ba, za a iya fuskantar ƙalubale “mu na gujewa guguwar juyin juya hali a Najeriya matuƙar gwamnati ba ta farka ta ɗauki matakan gaskiya na zahiri ba.”

Alamu na nuna batun neman ƙarin mafi ƙarancin albashi zai dakata zuwa wani lokaci don ‘yan ƙwadagon sun yaɗa gora sai komawa kan batun tsadar rayuwa.

Continue Reading

Kasashen Waje

Mun yi wa shugaba Biden bayani kan harbin da aka yi wa Trump – Pennsylvania

Published

on

Mun yi wa shugaba Biden bayani kan harbin da aka yi wa Trump - Pennsylvania

Mun yi wa shugaba Biden bayani kan harbin da aka yi wa Trump – Pennsylvania

Sakataren tsaron cikin gida na Amurka, Alejandro N. Mayorkas ya fitar da wata sanarwa game da harbin da aka yi a wurin yaƙin neman zaɓen tsohon Shugaban ƙasar Donald Trump a jihar Pennsylvania da safiyar yau.

A cikin sanarwar, Sakataren tsaron cikin gidan na Amurka Mayorkas ya bayyana cewa, “Ni da Daraktan ma’aikatar leƙen asiri Cheatle mun yi wa Shugaba Biden bayani game da harbin da aka yi yau a Pennsylvania. Ma’aikatar tsaron cikin gida (DHS) da Ma’aikatar Leƙen Asiri suna aiki tare da abokan aikinmu, masu kula da kiyaye doka don gudanar da bincike kan harbin.

KU KUMA KARANTA:Kotun Ƙolin Amurka za ta yanke hukunci kan takarar Donald Trump

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Muna Allah wadai da wannan tashin hankalin da kakkausar murya tare da yaba wa hukumar leƙen asiri bisa matakin gaggawar da ta ɗauka a yau. Muna tare da Shugaba Biden, tsohon Shugaba Trump, da yaƙin neman zaɓensu, kuma muna ɗaukar duk matakin da ya dace don tabbatar da tsaronsu. Kula da tsaron ’yan takarar Shugaban ƙasa da kuma taron yaƙin neman zaɓensu na ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da sashenmu ke ba da fifik

Tun farko Mai magana da yawun ma’aikatar leƙen asiri Anthony Guglielmi ya fitar da sanarwa a dandalin sada zumunta X, cewa, “Ma’aikatar leken asiri ta aiwatar da matakan kariya kuma tsohon Shugaban ƙasar yana cikin ƙoshin lafiya. Yanzu haka Hukumar tana gudanar da bincike, ta kuma sanar da Hukumar Binciken manyan laifuka ta FBI.”

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like