Abubuwan Da Ke Faruwa Sun Sabawa Hankali Da Tunani – Honarabul Yusuf Bala

0
312

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

WANI Dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna honarabul Yusuf Bala Ikara, bayyana abubuwan da ke faruwa sakamakon matsalolin tsaro da cewa sun sabawa Tunani da hankali.

Dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna karkashin tutar jam’iyyar APC Yusuf Bala Ikara, ya bayyana hakan a lokacin wata tattaunawa da wakilin mu a Kaduna.

Ya ce “hakika duk mai hankali da basira babu abin da ya dace ya ce sai ‘innalillahi wa’inna ilaihirraji’un’ domin kuwa lamarin da ke faruwa ya sabawa hankali da tunani baki daya, kuma wani lamari ne na bakin ciki da damuwa musamman ga al’ummar wannan yanki, yadda wadannan abubuwa kullum sai ci gaba kawai suke yi.”

“Na farko dai, mu ci gaba da yin addu’a kuma mu koma zuwa ga Allah, na biyu kuma ina yin jaje ga al’ummar Jihar Kaduna musamman na ganin yadda lamarin ya faru, ina mai jajantawa shugaban kasa da wadanda abin ya rutsa da iyalansu kuma ina mai jaje ga al’ummar karamar hukumar Giwa saboda abin ya faru da su har mutane suka rasa rayuka da dama da fatan Allah ya kawo karshe wannan lamarin, kasancewar kusan komai na kara ta’azzara ne a yanzu.”

Ya kara da cewa, abubuwan da ke faruwa ba za mu zargi kowa ba illa dai idan abu yazo a haka, ya dace daga bangaren Gwamnati ta zama ta na magance abu kafin faruwarsa ba wai sai ya faru ace za a dauki mataki ba, kullum akwai mutanen jami’an tsaro na ciki da na bayya ne su na ayyukansu ba mun Raina masu ba ne amma dai su kara kokari.

“Ya dace a fili ace Gwamnati na da labarin faruwar irin wadannan abubuwan a kuma dauki matakan magance su amma ban san abin da ke faruwa ba, amma a dan sanin da na yi kamata ace Gwamnati na da hanyoyin da za ta ji ba wai ayi irin wannan shirin ba amma Gwamnati ba ta Sani ba” a kai hari a harbi mutane a kwashi wasu duk ayi abin da aka yi amma Gwamnati ba ta da hanyar jin wannan labarin a gaskiya ya dace Gwamnati ta sake Daura dammara. Saboda daya daga cikin irin abin da ya sa mutane suka zabi wannan Gwamnatin ke nan ana ganin Gwamnatin baya ta gaza to, muma ta mu gashi ta zo muna yi wa Allah godiya ana bakin kokari amma dai a kara zage damtse, a mike tsaye a kara kokari a kan wannan lamarin.” Inji Shi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here