Gwamna Buni Ya Kaddamar Da Motoci 20 Ga Kamfanin Sufuri Na Jihar

0
335

Daga; Sani Gazas Chinade, Damaturu.

GWAMNAN Jihar Yobe Mai Mala Buni ya kaddamar da motoci kirar Toyota Hiace Bus masu daukar mutane 18 ga kamfanin sufuri na Jihar Yobe Line don samarwa al’ummar Jihar sauki dangane harkokin sufuri.

Da ya ke jawabi yayin kaddamar da motocin a gidan gwamnatin Jihar da ke garin Damaturu, Gwamna Buni ya ce wannan biki na kaddamar da wadannan motoci ya gudanar da shi ne da zimmar samar a sauki ga al’ummar Jihar wajen gudanar da harkokin su na yau da kullum.

“Kuma samar da wadannan motoci zai taimaka matuka gaya wajen rage yawaitar hadurran da ake samu lokaci zuwa lokaci saboda rashin kyan motocin sufuri.”

“Wadannan motoci na kamfanin sufurin Jihar Yobe line an samo su ne daga kamfanin Westwood Motors Limited cikin farashi Mai sauki ba tare da ruwa ba a kan zunzurutun kudi kimanin Naira
Miliyan 536,954,437,50.”

Don haka Gwamnan sai ya godewa kamfanin na Westwood Motors dangane da yadda ya hada kai da gwamnatin Jihar a kokarin da su ke yi na rage radadin wahalhalun da al’ummar Jihar suka yi fama da shi sakamakon rikicin Boko Haram da aka yi fama da shi a baya.

Baya ga samarwa kamfanin sufuri na Jihar Karin motocin gudanar da sufuri kuma har ila yau Gwamnan ya kuma samarwa Hukumar kula da dokokin sufuri a Jihar YOROTA kayayyakin gudanar da ayyukan su don ayyukan su, su gudana kamar yadda aka tsara.

Tun farko da ya ke jawabi kwamishinan ma’aikatar sufuri na Jihar Abdullahi Usman Kukuwa ya yabawa Gwamnan ne dangane wannan irin ayyukan alheri da ya gudanar ga ma’aikatar su ta sufuri.

Gwamnan ya kaddamar da jami’an Hukumar YOROTA kimanin 250 wadanda za su gudanar da ayyukan wannan Hukumar a cikin Jihar tare da kayayyakin gudanar da ayyukan su.

Leave a Reply