Ƙungiyar EU ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai wanda ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa 112

0
73

Babban jami’in harkokin wajen Tarayyar Turai Josep Borrell ya yi Allah wadai da kisan da Isra’ila ta yi wa Falasɗinawa 112 a lokacin da ake raba kayan agaji a Zirin Gaza da aka yi wa ƙawanya, yana mai cewa kisan sam bai dace ba.

“Na firgita da labarin sake yin wani kisan gilla a kan fararen hula a Gaza waɗanda ke neman agaji,” in ji shi a shafin X.

“Ba za a yarda da wannan kisa ba.”

Harbe-harben da Isra’ila ta yi, a cewar shaidu da likitoci, sun kuma jikkata Falasdinawa 760 waɗanda ke fama da yunwa.

Leave a Reply