Connect with us

Siyasa

Zan Hada Kan ‘Yan Najeriya Idan ku Ka Zabe Ni Shugaban Kasa – Bukola Saraki

Published

on

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

DAN takarar shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar (PDP), Sanata Dokta Abubakar Bukola Saraki ya tabbatarwa masu zaben dan takarar shugaban kasa (deliget) a Jihar Kaduna cewa in sun bashi damar ya zama dan takarar har nasara ta samu ya zama shugaban Najeriya, zai hada kan daukacin yan Najeriya domin a samu ci gaban da kowa ke bukata kuma ba zai ci amanar kowa ba.

Tsohon shugaban majalisar Dattawa ta kasa, Abubakar Bukola Saraki ya bayyanawa masu zaben dan takarar tare da sauran Jama’a a Kaduna haka ne a lokacin da ya je domin ya gana da su kuma ya bayyana masu kudirinsa ga daukacin al’ummar Kasar idan ya zama shugaban kasa.

Saraki ya ce sai da hadin kai sannan za a samu ci gaban ilimi, lafiya, Aikin Noma da kasuwanci da dukkan bangarori na rayuwa baki daya.

“Ni da kuke gani na nan zan yi maku aiki domin kasa ta ci gaba, na san matsalolin da kasa ke fuskanta kuma ina da kyawawan tsare-tsaren warware su baki daya”.

Ya fadakar da Jama’ar Jihar Kaduna cewa a lokacin da ya ke aikin Banki, ya san Kaduna sosai domin suna zuwa neman masu hulda da Bankin don haka ya san Kaduna. Akwai wuraren hada hadar kudi sosai don haka zai dawo da masana’antu kamar irinsu masaku da dimbin kamfanoni daban daban da suke a Jihar Kaduna, kuma ya yi musu alkawarin cewa zai yi maganin matsalar tsaron da ke addabar arewacin Najeriya domin sai da kwanciyar hankali da zaman lafiya ake samun ci gaban da kowa ke bukata.

Saraki ya kuma tabbatarwa da masu zaben dan takarar shugaban kasa cewa zai yi amfani da kwarewarsa ta zama Likita, mai’aikacin Banki, tsohon Gwamna Shekaru Takwas da kuma Sanata a matsayin shugaban majalisar baki daya, da ya kawo wa Najeriya da yan kasa gagarumin ci gaban da kowa zai yi farin cikin kasancewarsa dan Najeriya.

Daga cikin wadanda suka tofa albarkacin bakinsu a wajen wannan taron, akwai Sanata kuma tsohon minista Ibrahim Musa Kazaure, wanda ya shaidawa Jama’a cewa in dai yan Najeriya suna son ganin abin da ya dace na ingantar rayuwarsu, to su ba Sanata Abubakar Bukola Saraki amanar kuri’unsu domin mutum ne da kotun kolin Najeriya ta tabbatar da hukuncin cewa shi bai yi sata ba saboda haka amintacce ne.

Da yake magana da manema labarai, Sanatan yankin Kudancin Kaduna, Sanata Danjuma T. La’ah, cewa ya yi sun yi aiki tare da Bukola Saraki ya san shi sarai Idan ya ce zai yi kaza to hakan yake nufi lallai zai aikata, don haka mutum ne da za a bashi amana.

Daga cikin wadanda suka gabatar da jawabai a wurin taron domin yin kira ga masu zaben dan takarar shugaban kasa sun hada da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, mai girma Dallatun Zazzau Alhaji Dokta Ramalan Yero da shugaban PDP na Jihar Kaduna Mosta Felix Hassan Hyat da dukkan shugabannin Jam’iyyar na Jihar Kaduna da kuma dimbin yan tawagar Bukola Saraki.

An dai yi taro lafiya an kuma kare lafiya.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Siyasa

APC ta dakatar da ɗan Majalisa kan cin amana a Zamfara

Published

on

APC ta dakatar da ɗan Majalisa kan cin amana a Zamfara

Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta dakatar da Ɗan Majalisar Wakilai, Aminu Jaji bisa wasu zarge-zargen da ake yi masa na cin amanar jam’iyyar.

Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar APC na Jihar, Malam Yusuf Idris ne ya sanar da dakatarwar a wani taron manema labarai a Gusau a ranar Juma’a.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Jaji yana wakiltar mazaɓar Ƙaura-Namoda/Birnin-Magaji a Majalisar Wakilai a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Idris ya ce wasu zarge-zargen da ake yi wa Ɗan Majalisar sun haɗa da aikata rashin gaskiya da rashin zuwa tarurrukan jam’iyyar da kuma sauran ayyuka.

KU KUMA KARANTA: Kotun Najeriya ta bayar da umarnin dakatar da asusun banki fiye da dubu 1

Ya ce, matakin ya biyo bayan sanarwar dakatarwar da aka yi wa Jaji daga shugabannin jam’iyyar APC na mazaɓar Birnin-Magaji bisa zargin cin amanar jam’iyyar da dai sauran abubuwan da suka saɓa wa jam’iyyar.
Idris ya ce, “Kwamitin zartaswa na jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Birnin Magaji ne ya miƙa sanarwar dakatarwar zuwa hedikwatar jam’iyyar APC ta jihar.

Bayanai sun ce kwamitin zartaswar jam’iyyar APC na jihar ya gudanar da taron gaggawa a sakatariyar jam’iyyar da ke Gusau a ranar Juma’a 17 ga watan Mayu, 2024, inda aka gabatar da batun dakatar da Jaji ga ‘yan majalisar zartarwar jihar.

Continue Reading

Labarai

Tsohon gwamnan Katsina, Shema ya sauya sheƙa zuwa APC

Published

on

Tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shema, a hukumance ya koma jam’iyyar APC Mai mulki a jihar.

Shema, ya kasance gwamnan jihar a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2015, a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

Tsohon gwamnan ya yi rajista ne a ofishin jam’iyyar na mazaɓar Shema, ƙaramar hukumar Dutsin-ma, inda shugaban jam’iyyar na jihar, Sani Aliyu-Daura ya ba shi katin zama ɗan jam’iyyar APC.

Lambar katin Shema ta zama ɗan jam’iyyar ita ce: 26551.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Yobe za ta mayar da kwale-kwalen Dufuna mai shekaru 8,000 zuwa cibiyar yawon buɗe ido

Malam Aliyu-Daura ya yabawa Gwamna Dikko Raɗɗa da kuma tsohon gwamnan jihar Aminu Masari wanda ya gada, a bisa rawar da suka taka wajen ganin Shema ya sauya sheƙa.

Don haka ya tabbatar wa tsohon gwamnan cewa za a yi masa adalci kamar kowane ɗan jam’iyya.

Shugaban ma’aikata na Raɗɗa, Jabiru Abdullahi-Tasuri, shi ne ya miƙa katin zama ɗan jam’iyya ga Shema a madadin gwamnan a jiya Alhamis a Dutsin-ma.

Continue Reading

Labarai

Fusatattun matasa sun lakaɗawa kwamishina duka a wajen zaɓen fidda gwani

Published

on

Banji Ajaka, kwamishinan lafiya na jihar Ondo, ya gamu da fushin matasa a jiya Asabar yayin da ake gudanar da zaɓen fidda gwani na gwamna na jam’iyyar APC mai mulki a jihar.

Daily Trust ta gano cewa Dakta Ajaka, wanda ke Mazaɓar Ugbo 3, a ƙaramar hukumar, ana zarginsa da ɓoye takardar sakamakon zaɓen.

Shaidu sun tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa da suka yi da manema labarai, inda suka yi zargin cewa fusatattaun matasan ‘ya’yan jam’iyyar APC ne da ke adawa da tsarin da aka bi wajen gudanar da zaɓen.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka shaida lamarin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa rikicin ya faro ne lokacin da ‘yan ɗaya ɓangaren na jam’iyyar suka buƙaci ganin takardar sakamakon zaɓen na fidda gwani.

KU KUMA KARANTA:An yi jana’izar tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu

“Sun fusata ne suka buƙaci jami’in zaɓe ya ba su takardar sakamakon zaɓen sai kuwa ya ce ta na wajen Ajaka.

“Don haka suka yi masa duka a wurin, inda kuma garinsu ne. Jama’a sun fusata sosai da lamarin, inda rigimar ta ƙare a wajen.”

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Dakta Ajaka ya ce an zarge shi ne da riƙe takardar sakamakon zaɓen.

Ya yi bayanin cewa a lokacin da yake ƙoƙarin bayyana kansa, ’yan daban sun auka masa inda suka yi masa mugun duka.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like