Connect with us

Siyasa

Aiki Ja-Jawur Ya Samu ‘Yan Siyasa A Najeriya – Aliyu Waziri

Published

on

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

WANI fitaccen dan siyasa mai kokari wajen inganta rayuwar al’umma, Kwamared Aliyu Muhammad Waziri Santurakin Tudun Wada Kaduna da ake yi wa lakabi da dan marayan Zaki, ya fito fili ya bayyana cewa akwai babban aikin da ya samu yan siyasa kuma aiki ne Ja-Jawur a gabansu.

Kwamared Aliyu Muhammad Waziri, ya bayyana hakan ne a cikin wani shirin tattaunawa a kan al’amuran yau da kullum da suka shafi kasa ko duniya baki daya mai su na “Babban Gammo” na gidan rediyo da Talbijin na DITV da ke Kaduna Arewacin Tarayyar Najeriya.

Aliyu Waziri wanda shi ne shugaban kungiyar da ke koyawa matasa Noman zamani da ya kasance mai rike da Sarautun Gargajiya kala daban-daban wanda al’ummar Najeriya suka bashi, ya bayyana cewa idan aka yi tariyar abin da ya faru a shekarar 2015 lokacin da aka zabi shugaban kasan babu maganar jam’iyya domin ita maganar Jam’iyya duk wani lamari ne na ra’ayi kawai.

“Saboda haka ya na da kyau a duba me al’umma suke ciki wanda du ba da hakan ne ya kai ga aka zabi shugaban da ke kan mulki a halin yanzu ba tare da la’akari da batun Jam’iyya ba kawai dai mulki kawai ake son a dawo Arewa ba wata magana ba”, inji dan marayan Zaki.

San-Turakin Tudun Wada, ya ci gaba da bayanin cewa duk irin tururuwar da aka yi lokacin zabe a 2015 shi ne mulki kawai ya dawo Arewa ba maganar wata Jam’iyyar, illa mulkin dai ya dawo Arewa kawai.

“Saboda mulkin Najeriya na Arewa ne, amma saboda samun baragurbi ya sa mulkin ba a ga ne masa duk da ya dawo Arewa kuma dan Arewa ke yinsa”.

Ya kara da cewa ilimi, Zahiri da Siyasa duk wadansu abubuwa ne daban daban saboda haka ake kokari mutane su ga ne cewa akwai sauran shekarun da ya ragewa yan Arewa su kasance a mulki tun lokacin zamanin Obasanjo da ya kwashe shekaru Takwas, sai Umar Musa marigayi ya yi shekaru biyu, sannan Jonathan ya karba ya yi shekaru Shida a kan mulki kamin Buhari ya hau, duk da haka idan an kammala lissafi za a ga akwai sauran lokacin yan Arewa da ya rage su cikasa a mulkin Najeriya.

Idan hali ya yi zamu kawo maku ci gaban wannan doguwar tattaunawa da Aliyu Muhammad Waziri dan marayan Zaki ya yi. 

3 Comments

3 Comments

  1. salihu yusuf lailaba

    May 8, 2022 at 10:33 am

    Comment:kasuwanci

  2. salihu yusuf lailaba

    May 9, 2022 at 12:25 pm

    Comment:noma

  3. salihu yusuf lailaba

    May 9, 2022 at 12:26 pm

    Comment:sana.o i

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Siyasa

APC ta dakatar da ɗan Majalisa kan cin amana a Zamfara

Published

on

APC ta dakatar da ɗan Majalisa kan cin amana a Zamfara

Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta dakatar da Ɗan Majalisar Wakilai, Aminu Jaji bisa wasu zarge-zargen da ake yi masa na cin amanar jam’iyyar.

Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar APC na Jihar, Malam Yusuf Idris ne ya sanar da dakatarwar a wani taron manema labarai a Gusau a ranar Juma’a.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Jaji yana wakiltar mazaɓar Ƙaura-Namoda/Birnin-Magaji a Majalisar Wakilai a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Idris ya ce wasu zarge-zargen da ake yi wa Ɗan Majalisar sun haɗa da aikata rashin gaskiya da rashin zuwa tarurrukan jam’iyyar da kuma sauran ayyuka.

KU KUMA KARANTA: Kotun Najeriya ta bayar da umarnin dakatar da asusun banki fiye da dubu 1

Ya ce, matakin ya biyo bayan sanarwar dakatarwar da aka yi wa Jaji daga shugabannin jam’iyyar APC na mazaɓar Birnin-Magaji bisa zargin cin amanar jam’iyyar da dai sauran abubuwan da suka saɓa wa jam’iyyar.
Idris ya ce, “Kwamitin zartaswa na jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Birnin Magaji ne ya miƙa sanarwar dakatarwar zuwa hedikwatar jam’iyyar APC ta jihar.

Bayanai sun ce kwamitin zartaswar jam’iyyar APC na jihar ya gudanar da taron gaggawa a sakatariyar jam’iyyar da ke Gusau a ranar Juma’a 17 ga watan Mayu, 2024, inda aka gabatar da batun dakatar da Jaji ga ‘yan majalisar zartarwar jihar.

Continue Reading

Labarai

Tsohon gwamnan Katsina, Shema ya sauya sheƙa zuwa APC

Published

on

Tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shema, a hukumance ya koma jam’iyyar APC Mai mulki a jihar.

Shema, ya kasance gwamnan jihar a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2015, a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

Tsohon gwamnan ya yi rajista ne a ofishin jam’iyyar na mazaɓar Shema, ƙaramar hukumar Dutsin-ma, inda shugaban jam’iyyar na jihar, Sani Aliyu-Daura ya ba shi katin zama ɗan jam’iyyar APC.

Lambar katin Shema ta zama ɗan jam’iyyar ita ce: 26551.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Yobe za ta mayar da kwale-kwalen Dufuna mai shekaru 8,000 zuwa cibiyar yawon buɗe ido

Malam Aliyu-Daura ya yabawa Gwamna Dikko Raɗɗa da kuma tsohon gwamnan jihar Aminu Masari wanda ya gada, a bisa rawar da suka taka wajen ganin Shema ya sauya sheƙa.

Don haka ya tabbatar wa tsohon gwamnan cewa za a yi masa adalci kamar kowane ɗan jam’iyya.

Shugaban ma’aikata na Raɗɗa, Jabiru Abdullahi-Tasuri, shi ne ya miƙa katin zama ɗan jam’iyya ga Shema a madadin gwamnan a jiya Alhamis a Dutsin-ma.

Continue Reading

Labarai

Fusatattun matasa sun lakaɗawa kwamishina duka a wajen zaɓen fidda gwani

Published

on

Banji Ajaka, kwamishinan lafiya na jihar Ondo, ya gamu da fushin matasa a jiya Asabar yayin da ake gudanar da zaɓen fidda gwani na gwamna na jam’iyyar APC mai mulki a jihar.

Daily Trust ta gano cewa Dakta Ajaka, wanda ke Mazaɓar Ugbo 3, a ƙaramar hukumar, ana zarginsa da ɓoye takardar sakamakon zaɓen.

Shaidu sun tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa da suka yi da manema labarai, inda suka yi zargin cewa fusatattaun matasan ‘ya’yan jam’iyyar APC ne da ke adawa da tsarin da aka bi wajen gudanar da zaɓen.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka shaida lamarin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa rikicin ya faro ne lokacin da ‘yan ɗaya ɓangaren na jam’iyyar suka buƙaci ganin takardar sakamakon zaɓen na fidda gwani.

KU KUMA KARANTA:An yi jana’izar tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu

“Sun fusata ne suka buƙaci jami’in zaɓe ya ba su takardar sakamakon zaɓen sai kuwa ya ce ta na wajen Ajaka.

“Don haka suka yi masa duka a wurin, inda kuma garinsu ne. Jama’a sun fusata sosai da lamarin, inda rigimar ta ƙare a wajen.”

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Dakta Ajaka ya ce an zarge shi ne da riƙe takardar sakamakon zaɓen.

Ya yi bayanin cewa a lokacin da yake ƙoƙarin bayyana kansa, ’yan daban sun auka masa inda suka yi masa mugun duka.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like