Kungiyoyi 102 Sun Saya Wa Gwamna Matawalle Fom Din Tsaya Wa Takara

0
404

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

SAKAMAKON nuna yarda da kuma gamsuwa da jagorancin Honarabul Dokta Bello Muhammad Matawallen Maradun, Kimanin kungiyoyin 102 a Jihar Zamfara ne suka yi karo-karo suka tara naira miliyan 50 domin saya wa Gwamnan fom din takarar gwamna na karo na biyu da zai gudana a 2023.

A cikin wata takardar da aka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun sakataren yada labarai na Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara, Yusuf Idris Gusau, ya bayyana cewa bayyana Jindadinsu da godiya bisa karamcin da Kungiyoyin suka nunawa Jam’iyyar da Gwamnan Jihar.

Saboda haka ne jam’iyar APC ta Jihar Zamfara ke gayyatar dukkanin halatattun Ya’yan Jam’iyyar APC na Jihar zuwa wajen gangamin gabatar da takardar Kudin ga mai daraja, Gwamnan Jihar Zamfara, Honarabul Dokta Bello Muhammad Matawallen Maradun, karkashin jagorancin Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Honarabul Tukur Umar Danfulani.

Za a hadu a Babban Masallacin idi da ke Tudun Wada Gusau da karfe 8:00 na safe ranar Jumu’a 6/5/2022 inda za a taka zuwa Fadar Gwamnatin Jihar domin mika takardar kudin ga Gwamnan.

Shugaban Jam’iyyar ya kara da nuna godiyarsa ga Allah da al’ummar Jihar Zamfara akan irin Soyayya da su ke nunawa gwamnatinsu tare da rokonsu da su cigaba da baiwa gwamnatin goyon baya.

Haka zalika Shugaban ya nuna matukar godiyarsa ga wadannan kungiyoyin da sauran magoya bayan wannan gwamnatin tare da tabbatar masu da cewa Jam’iyyar APC ba za ta taba yar da su ba.

Leave a Reply