Zamfara: Yan Takarar Gwamna 3 Sun Bukaci Soke Zaben Fidda Gwani Na Jam’iyyar PDP

0
459

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

WASU yan takarar Kujerar Gwamnan Jihar Zamfara akalla mutane uku (3) wadanda suka hada da Ibrahim Shehu Gusau, Wadatau Madawaki da Aliyu Hafiz Muhammad sun garzaya kotu domin kalubalantar tsayar da Dauda Lawal Dare a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaben fidda gwani na Jam’iyyar ta PDP a Jihar.

Daya Dan takarar Ibrahim Shehu Gusau, a ta bakin babban lauyansa, Barista Ibrahim Ali Abubakar, a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Kaduna, ya bayyana cewa wanda yake karewa yana gaban babbar kotun Zamfara yana neman a soke zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar PDP daya gudana a ranar 25 ga watan Mayu.

Da yake karin bayani, Barr. Abubakar ya bayyana cewa rashin bin ka’ida, rashin daidaito, zamba, karya kundin tsarin mulkin jam’iyya, tanade-tanaden ayyukan zabe da dai sauran su a matsayin dalilan neman soke aikin.

“Muna da kwakkwarar hujja kuma mun gabatar da shaidun da ke nuna cewa atisayen da Adamu Maina Waziri ya yi, ya kasance da kura-kurai da dama ba tare da la’akari da tanade-tanaden da jam’iyyar ta yi na gudanar da zaben fidda gwani ba.

“Sai dai abin da Adamu Maina Waziri wanda shi ne shugaban kwamitin zaben ya yi, ya kasance cikakkiyar gadar tanade-tanaden kundin tsarin mulki, da dokokin zaben kasar nan na 2022 da sauransu.

“Saboda haka addu’armu ita ce, neman soke zaben gaba dayansa da umarnin kotu domin a sake yin wani sabon zaben a karkashin kulawar wasu marasa son zuciya wanda zai bai wa duk masu son tsayawa takara dama daidai da yadda jam’iyya da kasa suka tanadi dokoki da ka’idojin da ke jagorantar gudanar da zaben fidda gwanin” in ji Barista Ibrahim.

Idan dai za a iya tunawa Adamu Maina Waziri wanda shi ne Shugaban Kwamitin Zaben Gwamnan Jihar Zamfara na PDP ya bayyana Dauda Lawal Dare a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Mayu.

Halin da wasu ‘yan takara uku; Wadatau Madawaki, Aliyu Hafiz Muhammad da Injiniya Ibrahim Shehu Gusau ya ce an tafka magudi da rashin bin ka’ida, inda ya ce aikin ya sabawa ka’idojin jam’iyyar da kuma dokokin zabe.

Sai dai wadanda ake tuhumar ba su halarci zaman farko na karar da mai shari’a Aminu Bappa na babbar kotun tarayya da ke Gusau ya jagoranta ba.

Mai shari’a Bappa yayin da ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Yuli saboda rashin halartar wadanda ake kara da kuma lauyansu, ya umurci wadanda ake kara da su mayar da martani cikin kwanaki 30 da ikirari na mai kara Ibrahim Shehu Gusau.

Wadanda ake tuhumar sune; Adamu Maina Waziri, shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Zamfara, da Kanal Bala Mande (rtd). Haka kuma da hukumar Zabe (INEC) tare da Dauda Lawal Dare wanda aka bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben.

Leave a Reply