2023: Tinubu Ya Zabi Kabir Ibrahim Masari Daga Katsina A Matsayin Mataimakinsa

0
771

Daga; Rabo Haladu.

DAN takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana sunan Alhaji Kabir Ibrahim Masari a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na shekarar 2023.

Tinubu ne ya mika sunan Kabir Masari ne a matsayin wanda zai tsaya gabanin wa’adin da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta ba jam’iyyu na su mika sunayen ‘yan takararsu a zaben 2023.

Wasu majiyoyi daga bangaren Tinubu da Masari sun tabbatar da haka a yammacin ranar Alhamis.

Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC ya fito ne daga kauyen Masari da ke karamar hukumar Kafur a jihar Katsina kuma dan uwan ​​Rt. Hon. Aminu Bello Masari, Gwamnan Katsina ne.

Mataimaki na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya taba zama sakataren jindadi da walwala na kasa a jam’iyyar APC a lokacin Kwamared Adams Oshiomhole yana matsayin Shugaban Jam’iyyar na kasa.

Leave a Reply