Za Ta Ci Gaba Da Ba Da Tallafin Man Fetur Har Ta Sauka Daga Mulki

0
342

Gwamnatin Najeriya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta bayyana cewa tallafin da take bayarwa na man fetur zai ci gaba har nan da wata 18.

Ƙaramin Ministan Fetur Timipre Sylva ne ya faɗi hakan ranar Talata jim kaɗan bayan ya kammala ganawa da Buhari a fadar shugaban ƙasa, yana mai cewa za su nemi amincewar ‘yan majalisa nan gaba kaɗan.

Yanzu haka dai saura wata 16 wa’adi na biyu na gwamnatin ta Buhari na jam’iyyar APC ya zo ƙarshe.

Tun a ranar Litinin ne Ministar Kuɗi Zainab Shamsuna ta bayyana cewa gwamnati ta dakatar da maganar cire tallafin da ta tsara yi a watan Yunin 2022.

“Bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a ciki da wajen gwamnati, mun amince cewa ya kamata a jinkirta cire tallafin man fetur,” in ji ministan.

Ana sa ran gwamnatin za ta ƙara naira tiriliyan biyu da rabi a cikin kasafin kuɗinta don biyan tallafin na wata 18, idan aka yi la’akari da adadin da kamfanin mai na NNPC ya ce ya biya a 2021 na tiriliyan 1.7.

Sai dai babu tabbas game da abin da zai faru da tanadin sabuwar dokar Petroleum Industry Act, wanda ya ce wajibi ne gwamnati ta cire hannunta daga ƙayyade farashin man fetur.

Leave a Reply