Janar Aminu Chinade Ya Kaddamar Da Gidauniyar Tallafa Wa Marayu Da Marasa Galihu 

0
254

Sani Gazas ChinadeDaga Damaturu

A kokarin da ya ke yi wajen ganin ya tallafawa al’ummar sa wani Hafsan Sojan kasar nan Manjo Janar Aminu Shehu Chinade ya kaddamar da gidauniyar taimakawa marayu da yara marasa galihu a garin Chinade da ke karamar hukumar Katagum a Jihar Bauchi.

Manjo Janar Aminu ya sanar da  kaddamar da wannan gidauniya ne a wajen wata liyafar girmamawa da al’ummar garin na Chinade suka shirya masa a kwanakin baya bisa Karin girma da ya samu daga matsayin Birgediya Janar ya zuwa matsayin Manjo Janar a kwanan nan, bikin da aka gudanar a babbar makaranatar Firamare ta (Central Primary School ) Chinade.

Hafsan Sojan ya godewa al’ummar sa bisa ga shirya ma sa wannan liyafa da suka yi, yadda ya jaddada musu cewar, ya yi alkawarin ci gaba da hidimta musu  da ma sauran al’ummar kasar nan in Allah SWT ya so.

Dangane da wannan gidauniya kuwa Janar din ya bada gudummawar kimanin Naira Miliyan 2 domin kafa wannan gidauniya wadda hakan ne ya bada dama ga sauran al’ummomin suka Tara kudaden da ba su gaza Naira Miliyan 3.5 ba wadda adadin kudin da aka tara a wannan gidauniya ya kai minzalin Naira Miliyan 5.5 nan take.

Da ya ke jawabi ya yin taron wannan liyafa shugaban taron Ambasa Jibrin Dada Chinade ya yabawa Janar Aminu bisa ga kwazon sa a wajen aiki wadda bisa ga hakan ne har ta kai shi ga samun Karin girman da ya ke a yanzu.

Don haka ne ya kirayi al’umma da su ci gaba da yi masa addu’ar samun ci gaba da nasara da gamawa lafiya a gidan soja da ma sauran al’amuran da ya sa gaba.

Ambasa Dada Chinade ya kuma kwatatanta Janar din a matsayin babban jigo ga al’ummar yankin sa na Chinade, yadda ya roke shi da ya ci gaba da irin ayyukan alheri da kuma gudummawar da ya ke baiwa al’ummar sa tare da jajircewa don ganin ci gaba mai daurewa na gudanuwa a wannan yanki nasa da kasar Katagum, Jihar Bauchi da ma kasa baki daya.

Ambasada  Chinade ya kuma kirayi dukannin al’ummar yankin na Chinade da su yi koyi da irin wannan hobbasa da janar Aminu Ya yi na kokarin assasa abin alkhairi ga al’ummar sa.

Al’ummar Chinade daga ko’ina sun halarci wannan taro na karrama Manjo Janar Aminu Shehu Chinade, kana wasu abokan arziki daga yankin Katagum, Jihar Bauchi kwata da kasa baki daya su ma sun halarci wannan  taron liyafa da kungiyar (Chinade Development Agenda) CDA ta shirya.

Leave a Reply