Za A Iya Amfani Da Matakan Tattaunawa Da Kera Makaman Cikin Gida Domin Magance Matsalar Rashin Tsaro – Buratai

0
330

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

TSOHON babban hafsan sojin kasa (COAS), Laftanar Janar Tukur Yusufu Buratai (rtd), ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro a kasar Najeriya ya kasance tamkar wani dodo mai rikitarwa wanda ba lallai ne sai ta hanyar yaki da kai hari za a iya magance shi ba domin za a iya hanyar ɗaukar mataka tattaunawa da kera kayan aikin soja na gida.

Laftanar Janar Tukur Yusufu Buratai, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wata lacca mai taken, “Siyasa da rashin tsaro a Najeriya: Hanyar ci gaba” a wani taron yini guda kan harkokin tsaron kasa a gidan tarihi na Sardauna dake Kaduna a ranar Asabar 11 ga Yuni, 2022.

A cewarsa, ya kamata irin wadannan hanyoyin da ba na yaki ba da suka hada da tattaunawa bisa hadaddiyar hanyoyi, da za su kawo karshen rashin tsaro ta hanyar hada shugabannin gargajiya da na addini, kafofin yada labarai, tsaro da hukumomin leken asiri domin warware matsalar da ake fuskanta.

Ya ce, “ya kamata a ci gaba da wayar da kan jama’a kan rawar da ya kamata su taka domin kawo karshen rashin tsaro a matsayinsu na masu ruwa da tsaki,” in ji shi.

Ya kuma ba da shawarar sake farfado da masana’antun tsaron Najeriya (DICON), da kyautata jin dadin jama’a da damar da kayan aiki ga ‘yan sanda, tare da kafa rundunar kan iyakokin kasa kamar yadda ake yi a sauran kasashen duniya.

Mai rike da sarautar gargajiyan, ya kuma shawarci ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA) da su hada kai da kuma yi amfani da duk wata hanya da za a bi wajen dakile kayan da ake kaiwa ‘yan ta’adda.

“Ya kamata jihohi da kananan hukumomi su rufe wuraren da ba na gwamnati ba don hana ’yan tada kayar baya da kuma ‘yan fashi da ke yawo cikin walwala.

“Mayaka a kullum suna cikin daji ko da sojoji sun kawar da shugabanninsu da sauran su, za su ci gaba da daukar ma’aikata, batun tattaunawa yana da matukar muhimmanci, idan ka kawar da wadanda ke cikin daji, yaya shugabannin siyasarsu da masu daukar ma’aikata?” Ya tambaya cike da rarrashi.

Da yake karin haske kan mahimmancin tattaunawa, ya ce ya yi daidai da tsarin da babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Gumi ke gabatarwa.

“A nan ne nake yabawa Sheikh Gumi bisa wannan yunkuri nasa, kashi daya bisa uku na fadan soja ne, shi yasa sauran za su kasance ta hanyar tattaunawa, wanda dole ne mu samu wannan mafita kuma wannan ne lokacin da ya dace don ganin an shawo kan lamarin.” Inji shi.

Leave a Reply