Hajj 2022: Jihar Kaduna Za Ta Yi Jigilar Maniyata Aikin Hajjin Bana 2491

1
267

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

AN yi kira ga maniyyatan aikin Hajjin baba a jihar Kaduna da su bi ka’idojin addinin Musulunci a yayin da suke gudanar da aikin hajjinsu

Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna, Malam Yakubu Al-Rigasiyyu ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga maniyyatan da suke shirin tantancewa a sansanin alhazai da ke Mando, Kaduna.

A cewarsa, yana da kyau su nemi ilimin da ya dace na dukkan ayyukan hajji domin su samu nasarar gudanar da aikin hajjin.

Ya ce, “Jikin aikin hajjin bana yana kan gaba, ba zai dace ku taru a birni mai tsarki ba kuma ba ku yi aikin hajji da kyau ba, yana da kyau ku hadu da jami’an da suka kware da ilimi domin su jagorance ku kan dukkan ayyukan ibada da ake tsammanin ku yi”.

Da yake karin haske, jami’in hulda da jama’a na hukumar Sani Anchau ya ce kimanin mahajjata 2491 ne za a yi jigilar su zuwa kasa mai tsarki ta hanyar kamfanonin jiragen sama na Azman.

Ya bayyana cewa, maniyyatan da za a yi jigilar su a jirgi za a fitar da su daga kananan hukumomi daban-daban.

“Saboda annobar Cutar Korona, ana sa ran alhazai za su samu allurai uku na allurar rigakafin Cutar Korona wanda shi ne babban ka’idojin bayar da biza, don haka sai wadanda aka shirya bizarsu a wani lokaci, ba tare da la’akari da kananan hukumominsu ba, za a duba su kuma a dauke su ta jirgin sama zuwa kasa mai tsarki”.

Amma Anchau ya ba da tabbacin cewa, duk biza za su kasance a shirye kuma za su kasance a cikin lokacin da ake sa ran jirgin.

Sansanin aikin hajjin da ba a yi amfani da shi ba tsawon shekaru biyu saboda annobar korona, an gyara shi tare da sanya muhallin cikin yanayin kwanciyar hankali domin maniyyatan su zauna kafin tashin jirgi.

1 COMMENT

Leave a Reply