‘Yan wasan Man City bakwai sun tafi jinya

0
126

Rahotanni suna nuna cewa kusan ‘yan wasa bakwai na Man City ba za su samu damar buga wasan da ke gaban ƙungiyar ba na ranar Lahadi mai zuwa, wato wasansu da Arsenal a Gasar Firimiya.

Arsenal ce dai ke jan ragamar teburin gasar Firimiya, inda take saman Liverpool wadda duk da cewa su biyun suna da maki 64, bambancin yawan kwallaye ya sa ta shige gabanta.

Kasancewar Man City na da maki 63, a mataki na uku, ya sa wasan nasu da Arsenal yana da matukar muhimmanci, domin kuwa zai iya kai su ga hayewa saman teburin idan har ita ma Liverpool ba ta yi nasara ba.

Sai dai kash, ƙungiyar da ke rike da kofin Firimiya na bara, tana fuskantar babban ƙalubalen yiwuwar rashin manyan ‘yan wasanta da za su taimaka mata ta yi galabata.

Jerin dakarun ‘yan wasan Man City da ake tsoron ganinsu a wasan na gaba sakamakon tafiya jinya sun hada da Kevin De Bruyne, da John Stones, da Kyle Walker, da Manuel Akanji.

“Waɗannan ‘yan wasa sun samu raunuka ne a wasannin da suka buga wa kasashensu na asali, a jerin wasannin sada zumunta na ƙasa-da-ƙasa da aka kwashe makonnin ƙarshen watan Maris ana gudanarwa.

“Yawancin ‘yan wasan ‘yan baya ne da ke taimakon kungiyar tsaron baya. Ammma kuma akwai Kevin De Bruyne wanda zai zama babban rashi ga karfin ƙungiyar na kai hari.

Sannan kuma akwai tsoron rashin wasu manyan ‘yan wasan kamar Jack Grealish da Matheus Nunes wanda ba dole su iya dawowa buga wasa ba a ranar ta Lahadi.

Shi ma mai tsaron raga, Ederson zai iya rasa wasan na gaba, sakamakon cigaba da jinyar da ya fara bayan da aka cire shi a wasansu da Liverpool saboda jin rauni, tun makonnin baya.

KU KUMA KARANTA: Man United ba za ta sayo Bellingham na Real Madrid ba

Nunes wanda ɗan Portugal ne, ya samu rauni inda aka cire shi a wasan sada zumunta da ya buga wa kasar tasa. Shi kuwa De Bruyne da ma yana fama da ciwon ciki ne.

A tarihin karawar Man City da Arsenal na baya-bayan nan, City ce ta fi samun galaba, musamman a wasannin da suka buga a gidanta da ke filin wasa na Etihad. Amma dai a wasansu na farko na kakar bana, Arsenal ce ta doke City da ci 1-0.

Wannan ne ya sa dole koci Guardiola ya sha jinin jukinsa yayin zuwa wannan wasa ba tare da dakarun ‘yan wasansa ba, musamman ganin cewa akwai wasanni gasar FA da Chelsea, da kuma na Zakarun Turai da Real Madrid.

Leave a Reply