Yan Takarar Majalisar Wakilai Sun Samu Nasara Ba Hamayya A Jihar Zamfara

0
349

Daga; Imrana Abdullahi.

BAYANAN da muke samu daga Jihar Zamfara na cewa yan takarar majalisar wakilai ta tarayya guda shida daga Jihar Zamfara sun samu nasarar tsayawa takarar ba tare da wata hamayya ba.

Sun dai tabbata da samun wannan nasarar ne a lokacin wani zaben fitar da Gwanin da ya gudana a Jihar.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun mai magana da yawun jam’iyyar APC a Jihar Zamfara Yusuf Idris Gusau.

Wadanda suka samu nasarar sun hada da Abba Ahmad Sani da zai wakilci kananan hukumomin Bakura/Maradun, Honarabul Aminu Sani Jaji kananan hukumomin Kaura/Birnin Magaji, sai Isa Muhammad Anka kananan hukumomin Mafara/Anka a majalisar wakilai ta kasa.

Sauran sun hada da Honarabul Sanusi Garba Rikiji Gusau/Tsafe, Alhaji Umaru S/Fada kananan hukumomin Shinkafi/Zurmi da Alhaji Ahmad Usman Gummi kananan hukumomin Gummi/Bukkuyum.

Yayin da tsohon dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Maru/Bungudu, Honarabul Abdulmalik Zubairu Zannah ya samu nasara a kan Alhaji Abdulrahaman Tumbido da Dakta Bashir Mohammed Maru inda ya samu nasarar tsayawa takarar.

Zaben fitar da yan takarar dai ya samu nasarar kammaluwa ne cikin yanayin kwanciyar hankali da natsuwa a gaban masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da kuma jami’an hukumar zabe ta kasa da jami’an jam’iyyar APC daga hedikwatar su ta kasa.

Reshen jam’iyyar na Jihar Zamfara ya yabawa yayan jam’iyyar bisa bin doka da oda da suka yi a lokacin zaben da kuma bayan zaben baki daya.

Shugaban jam’iyyar ya tabbatarwa da daukacin mambobinsa bayar da cikakkiyar dama ga kowa domin samun ribar Dimokuradiyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here