Nentanwe Ya yi Nasarar Lashe Zaben Fidda Gwani Na APC A Matsayin Dan Takarar Gwamnan Filato

0
285

Daga; Isah Ahmed, Jos.

WAKILAN Jam’iyyar APC masu zaben yan takara na Jihar Filato, sun zabi Dokta Nentanwe Yilwarda a matsayin Dan takarar kujerar Gwamnan Jihar a zabe mai zuwa na shekara ta 2023. Wakilan sun zabi Dokta Nentanwe ne da kuru’u 803, a wajen da aka gudanar da zaben a Reyfield kusa da garin Jos a ranar Alhamis data gabata.

Shugaban kwamitin da ya gudanar da zaben Honarabul Habu Ajiya ya bayyana cewa mutane 9 ne suka shiga wannan takara. A yayinda 5 daga cikinsu suka mika takardar janyewa daga takarar kafin a gudanar da zaben.

Ya ce wadanda suka janye daga wannan takara sun hada da Sunday Garba Biggs, Dokta Sarpiya Danyaro, Sanaya Hezekiah Dimka, Dokta Patrick Dakum da kuma Arch Fitka.

Ya ce sakamakon sauran yan takarar da suka shiga wannan takara sune Garba Pwul ya sami kuru’u 2 da Farfesa Sunny Tyoden da ya sami kuru’u 25 da kuma Honarabul Victor David Dimka da ya sami kuru’u 7.

Leave a Reply