Connect with us

Uncategorized

‘Yan Majalisa Na Da Ikon Tabbatar Da Dokar Tsarin Zaben ‘Yar Tinke-Dokta Nasirudeen

Published

on

Daga Isah Ahmed, Jos

Dokta Nasirudeen Usman, shi ne  Daraktan   Sashin horar da manyan ma’aikata na Sojoji da   manyan jami’an tsaro, na Cibiyar Nazarin Dabarun Mulki ta Kasa [NIPSS] da ke Kuru,  a Jihar Filato. Kuma masani  kan harkokin shari’a a Najeriya. A wannan tattaunawa da ya yi, da wakilinmu ya bayyana cewa ko Shugaban Kasa, bai sanya hanu kan dokar nan ta tsarin zaben ‘yan tinke, da ake ta dambarwa a kai ba. ‘Yan majalisar dattijai da ‘Yan majalisar wakilai ta tarayya, zasu iya tabbatar da wannan doka.

Ga yadda tattaunawar ta kasance

GTK: Mene ne zaka ce kan batun dokar nan, ta zaben ‘yan tinke  da ake ta dambarwa a kai?

Dokta Nasiruddeen:Maganar tsarin yadda jam’iyyu suke  fitar da ‘yan takararsu, doka ta basu hanyoyi guda biyu ne.

Jam’iyyu suna da zabi ko dai su fitar da ‘yan takararsu ta haryar    zaben ‘yan tinke, wadda wasu suke kira  kato bayan kato. Ta yadda dukkan ‘yan jam’iyya, wadanda suke da katin jam’iyyar zasu fito su zabi, wanda suke so ya yiwa wannan jam’iyya takara.

Ko kuma su bi hanyar zaben wakilan jam’iyya, wadda ake kira Deligete. Wato wasu ‘yan jam’iyyar da ake zabe,  a matakin Unguwa  da  matakin Karamar Hukuma da matakin Jiha, domin  su taru su zabi ‘yan takarar wannan jam’iyya.

To, matsalar da ake samu a nan  ita ce, zaka ga jam’iyyu sun  fi amfani da wannan tsari na Deligete. Kuma  zaka samu a cikin ‘yan takarar da suka tsayawa wannan jam’iyya, zaka sami wani ko shi ne yafi kowa lalacewa,  cikin ‘yan takarar, idan yana da kudi zai iya sayen dukkan wadannan Deligete. Zaka ga mafiyawan mutanen jam’iyyar ba shi suke so ba,  amma ya bayar da  kudi ya ci wannan zabe.

Ko kuma ace gwamnati a jiha ko a Karamar Hukuma, su ce dole ga wanda suke so, ya tsaya takara saboda haka dole a tursasawa  Deligete su zabi wannan dan takara.

Kuma babbar matsalar  su kan su Deligete din, ba zabarsu ake yi ba. Ana zama ne wadanda suke ganin sune masu ruwa da tsaki, ko gwamna ko Shugaban Karamar Hukuma su ce wane da wane sune shugabannin jam’iyya. Kaga baki daya, an dauke ruhin damakoradiya a nan.

 Don haka idan da aka zo babban zabe, sai dai mutane su zabi wanda yafi dama dama, cikin rubabbun da jam’iyyu suka tsayar masu takara.

Wannan abin shi ne ya jawo cece kuce ake ganin cewa, idan ana son ayi damakoradiyar ne a fara tun daga zaben ‘yan takarar jam’iyyu.

Wato ya zamanto wajen tsayar da ‘yan takara na jam’iyyu, ba mutum daya ko biyu ko uku ne zasu fitar da ‘yan takara ba. Jama’a magoya bayan jam’iyya ne za a basu dama, su zabi ‘yan takara.

Don haka ake ta dambarwa, tsakanin ‘yan majalisa da Shugaban Kasa. Inda ‘yan majalisar tarayya na Sanatoci da na tarayya, suke cewa ayi zaben kato bayan kato.

GTK: Ganin Shugaban Kasa bai sa hanu kan wannan doka ta zaben ‘yan tinke ba, kana ganin ‘yan majalisa suna da damar su tabbatar da wannan doka?

Dokta Nasiruddeen: A tsarin mulkin Najeriya  zasu iya. Domin yadda yin doka yake a kasar nan, abu ne guda biyu dole sai sun faru. Wato sai majalisun nan guda biyu, na Dattijai da na Wakilai na tarayya sun yarda cewa abu kaza da abu kaza ne, zai zama doka. Idan sun amince a tsakaninsu sai su turawa Shugaban Kasa. Shi kuma ya amince ya sanya hanu, kafin abin ya zama doka. Idan aka kai masa yana da damar ya ce abu kaza da abu kaza da aka kawo,  bai yarda da shi ba, saboda dalilai kaza da kaza, ya mayar masu. Idan bai yi haka ba, har  kwanaki 30, zasu yi amfani da damar da tsarin mulki, ya basu su kawar da wannan dama, ta Shugaban Kasa su zartar da wannan doka.

To yanzu halin da ake ciki game da wannan doka, Shugaban Kasa ya yi korafe korafe ya mayarwa masu,  ya ce su sake nazari.

A cikin korafe korafen Shugaban Kasa akwai yanayin yadda Kasar nan ta tsinci kanta a ciki, na rashin tsaro da makudan kudaden da za a kashe, wajen gudanar da wannan zabe.

Babu shakka akwai wadannan abubuwa da Shugaban kasa ya fada, amma ni  kullum abin da nake fada, shi ne idan matsala ta taso sai a sanya ta a ma’auni, aga wanne ne yafi illa? Shin Illar da za a yiwa damakoradiya ta hanyar dauki dora ne ko kuma illar wahalar da za a sha idan aka yi zaben kato bayan kato tafi?.

 Sai a gwada aga wanne ne yafi, Idan aka ga wanda yafi sai a dauka.  

Amma dai abu mai mahimmanci, zaben nan na shekara ta 2023 ya karato, don haka dole ne mu yi kokari mu san abin da zamu yi, na tsarin doka. Domin hukumar zabe ta kasa INEC, ta sami isasshen lokaci zata tsara abubuwan ta.

Yanzu dai  Shugaban Kasa ya mayar masu, zasu iya cewa sun yi nazari kan korafe korafen da ya yi  sun yi kwaskwarima  ya sanya hanu, idan kuma suka ce su suna nan, kan matsayarsu zasu iya sake mayar masa, idan bai sanya hanu ba, cikin kwana 30, zasu iya tabbatar da wannan doka.

GTK: Ya ya kake ganin yanayin tafiyar harkokin Shari’a a wannan gwamnati?

 Dokta Nasiruddeen: Wato ni a fahimtata, idan aka sami matsala a cikin al’umma, ko gyara  yana shafar kowanne Bangare. Kasar nan yanzu muna cikin wani hali na rudani, musamman a siyasance. Idan aka sami irin wannan, dole wannan al’amari ya shafi kowanne bangare.

Babbar matsalar ita ce bangaren shari’a, wanda  shi ne ake gani  a matsayin yaki na karshe.  Domin komai lalacewar al’umma,  ana sa ran  idan aka yiwa mutum, wani abu wanda ba dai dai ba, idan yaje sashin shari’a, za a kwatar masa hakkinsa.

To, a  nan zan iya cewa ana kokartawa, gwargwadon hali a wannan gwamnati. Amma  ina tabbatar maka, gurbacewar  al’ummarmu bai bar bangaren shari’a ba.

GTK: Ana  kukan cewa akwai wasu manya a Kasar nan  da suke  gaban kotuna kan tuhumar aikata laifuffuk,a amma an ji shuru kan irin wadannan shari’o’ mene ne kake ganin ya kawo haka?

 Dokta Nasiruddeen: Wato abubuwa da yawa ne suke kawo wannan abu. Yanzu  kasar nan  da zarar an yi zargin wani ya yi laifi, musamman saboda yadda cin hanci da rashawa ya addabi al’umma. Don haka mutane da dama, suna bukatar suga an yankewa wannan mutum, da ake zargi hukumci an kai shi gidan yari, ko kuma wani abu makamancin haka.

 To amma ita shari’a a wajen ta, zargi daban hukumci tabbatar da zargi daban. Sai an yi zargi an bi matakan da ake tabbatar da zargin, idan an tabbatar da zargin nan, sannan hukumci ya biyo baya.

To inda ake samun matsalar, matakan da ake bi, na tabbatar da zargin  sune ke da matsala. Kuma wannan yana da nasaba ne da irin tsarin shari’ar da muke bi. Duk da akwai gyare gyare da aka yi, daga baya bayan nan, domin a cire wasu abubuwa na yadda ake yi a tabbtar da mai laifi. Misali akwai sabon kundi wanda tun a shekara ta 2015, aka fito da shi wanda ya kun shi doka da aka yi a gwamnatin tarayya,  kuma  jihohi da dama sun fara aiki da wannan kundin doka.  Manufar wannan kundin doka, shi ne a sassauta matakan da ake bi, na tabbatar laifi ga wanda ake zargi.

Hukumar ‘yan sanda ko hukumomin yaki da cin hanci da rashawa kamar EFCC ko ICPC. Sune idan an kawo korafi a wajensu, ko kuma  kan tafiyar da aikinsu,  idan suka gano an yi wata barna, zasu dauki matakai da bincike don ganin an tabbatar da wannan laifi, da ake korafi da shedu  su gabatarwa kotu.

 Idan ba abi wannan ba, ita kotu  ba zata ce, da zarar an kawo wanda ake tuhuma da aikata laifi, nan take aje a garkame shi ba.  Matsalar da ake samu ke nan.

Kuma musamman sha’ani na tuhuma kan cin hanci da rashawa.  Zamani ya kawo sarkakiya  na tabbatar da wadannan laifuffuka. Kuma wadanda ake zargin nan, suna da kudaden da zasu amfani da su, don kawo cikas kan matakan da ake bi wajen tabbatar da zargin da ake yi masu. Wannan wani abu ne wanda ba karamin aiki ne ba.

GTK: Wadanne hanyoyi ne kake ganin za abi a warware wadannan matsaloli?

 Dokta Nasiruddeen: Ni a ra’anyi duk wanda aka ce ya saci kudin gwamnati har Naira miliyan 100, ko sama da haka. Idan kaje kace kana bincikensa, ina tabbatar maka zai iya salwantar da rabin wannan kudi, domin yaga cewa ba a hukumta shi ba. Kuma ba kowanne mutum ne zai kawar da kai, daga karbar  kan cin hanci da rashawa ba a wannan lokaci da muke ciki.

Don haka ni a ra’ayina, abi matakan  kada  a bar barnar ta faru. Domin idan a yau aka dada tsaurara hanyoyin da ake bi, wajen kashe kudaden gwamnati. A tabbatar cewa duk Naira daya da aka kashe ta gwamnati   an san inda aka kashe ta. Kaga ba za a zo kan cewa ana zargin wani ba, kuma ana son a bincike shi.

Muna da wata Hukuma da gwamnatin tarayya ta kafa, wadda ake kira Fiscal Responsibility. Wannan hukuma ce da aka kafa ta domin tabi, diddigin yadda ake tsarin kasafin kudi da yadda ake sakin wannan kudi da yadda ake aiwatar da ayyuka.

Ya kamata wannan hukuma ta rika bibiya, tun daga matakin tsara kasafin kudi, da yadda ake gudanar da aikin  da aka bayar da yadda aka kashe kudin.

Ina tabbatar maka, idan da an baiwa  wannan Hukuma  karfin da ya kamata a doka,   tayi aikin ta kamar yadda doka ta ce. Wallahi Hukumomin EFCC da ICPC zasu  rasa aikin da zasu yi. Kuma da yawa a matakan jihohi, gwamnoni sun kafa irin wadannan hukumomi. Amma ba a bari su yi aikin da ya kamata.

 Don haka ni a ra’ayina ayi abin da za a hana barna, kafin ace a bari sai mutum ya aikata barnar, sannan ace za a kama mutum ayi bincike.

GTK: Karshe wanne sako ne kake da shi zuwa ga al’ummar Najeriya?

 Dokta Nasiruddeen: Yadda muka tsinci kanmu a kasar nan, abu ne mai ban tsaro da takaici. Duk ni’imar da Allah yake yiwa al’umma a duniya, Allah ya yiwa kasar nan. Amma kullum muna cikin waiyo waiyo.

 Ni a ganina wannan hali da muka shiga, ba abu ne da za a dora shi ga shugabanni kadai ba. Ya kamata mu a matsayinmu na ‘yan kasa, mu dubi kanmu mu dubi mu’amalarmu da iyalanmu da sauran abokanan zamanmu. Kuma mu sani babu wanda zai zo, ya gyara mana kasarmu dole mu ne zamu tashi mu hada hanu mu gyara kasar nan.

Ni ɗan jarida ne mai zaman kansa. Mawallafi kuma mai sharhi a lamarin yau da kullum.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Addini

Ranar Lahadi ce 1 ga watan Muharram – Sarkin Musulmi

Published

on

Ranar Lahadi ce 1 ga watan Muharram - Sarkin Musulmi

Ranar Lahadi ce 1 ga watan Muharram – Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad III, ya bayyana cewa gobe Lahadi ce za ta zama 1 ga watan Muharram na sabuwar shekarar Musulunci ta Hijira 1446.

Shugaban kwamitin da ke bai wa Sarkin Musulmi shawara kan harkokin addini, Farfesa Sambo Wali Junaid ne bayyana hakan a ranar Juma’a.

Farfesa Junaid ya ce kwamitin haɗin gwiwa da kwamitin ganin wata na Najeriya sun tabbatar ba a samu ganin watan Muharram na shekarar 1446 a ranar Juma’ar ba, abin da ke nuna ranar Asabar za ta zama 30 ga watan Zhul Hijja na shekarar 1445.

KU KUMA KARANTA: A fara duban watan sabuwar shekarar Musulunci – Sarkin Musulmi

“Sakamakon haka, Asabar [6 ga watan Yuni] ta zama 30 ga watan Zulhijja 1445…Lahadi kuma [7 ga Yuni] ta zama 1 ga watan Muharram 1446,” a cewar shugaban kwamitin ganin wata na fadar sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali cikin wata sanarwa.

“Sarkin Musulmi na taya Musulmin Najeriya murna [sabuwar shekara] da kuma roƙa musu alheri da taimakon Allah,” in ji sanarwar.

Sarkin Musulmin ya roƙi jama’a su ci gaba da addu’ar zaman lafiya da samun ci gaba a ƙasa baki ɗaya.

A tsarin Musulunci, kowane wata kwana 29 ne amma idan aka kasa ganin jaririn sabon wata akan cika watan zuwa kwana 30.

Continue Reading

Addini

Biyan kuɗin shiga Itikafi a Masallatai bidi’a ce — Sheikh Maqari

Published

on

Babban Limanin Masallacin Juma’a na Ƙasa, Farfesa Ibrahim Maqari ya yi tir da tsarin da wani Masallaci a Legas ya fito da shi na biyan kuɗi kafin mutum ya yi ibadar Itikafi a cikinsa.

Limamin ya bayyana ɓacin ransa na wannan sabon abu da Masallacin ya fito da shi ne tare da yin sharhi mai tsawo kan haka a yayin tafsirinsa da ya ke yi a Babban Masallacin Juma’a na Ƙasa da ke Abuja.

Shehun Malamin ya kwantanta wannan mataki da masallacin na Legas ya fito da shi a matsayin wata sabuwar fitina a addini wacce ta fi kowacce bida’a muni a wannan zamani.

Wanda a cewarsa hakan zai iya haifar da fushin Allah kan wannan al’umma saboda kasuwantar da ɗakinSa ne wanda wasu addinai ke yi.

“Masallaci ɗakin Allah ne kuma da zarar mutum ya shiga, duk wani girma da ɗaukaka da muƙami da matsayi ya kare bakin kofa inda ya ajiye takalminsa.

“Duk wanda ke cikinsa daidai yake da kowa ba tare da banbancin mai shi da maras shi ba na dukiya ko matsayi.

“A inda zai iya zama a ko’ina kuma kusa da kowa. Amma sa kuɗi zai buɗe kofar nuna banbanci da matsayi wanda hakan ba musulunci bane,” in ji shi.

A yayin da yake amsa tambayoyi a ƙarshen tafsirin a inda wani ya bayar da hujjar Masallacin na karɓar kudi don kula da shi ne da kuma sayen Man dizel.

Sai Malam ya amsa da cewa hakan bai halarta ba.

“Sai dai in wasu ɗakuna aka ware a cikin masallacin wanda mutum zai kama ya zauna don yin Ibada wanda hakan ya halarta ko kuma kuɗin da ake biya na amfani da banɗakuna ne da za a shiga don biyan buƙata wanda da su za a kula da tsafta da gyaransa da kuma ma’aikata.

“Amma in don a shiga cikin Masallacin a yi Ibada ne kamar Itikafi ne sai an biya saboda a taƙaita yawan mutane, wannan bai halarta ba.

KU KUMA KARANTA: Malaman addini a Malawi sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da auren jinsi

“Wanda kuma dole ne musulmai su haɗu su yaƙi wannan bida’a wacce ta fi duk wata bida’a da wasunsu ke ta suka muni saboda abin da hakan zai haifar a nan gaba,” in ji shi.

Jaridar Aminiya ce ta ba da rahotan Masallacin Juma’a na unguwar masu hannu da shuni na Lekki da ke Jihar Legas ya saka Naira 130,000 ga duk mai son yin Itikafi a cikinsa wanda hakan ya haifar da cece-ku-ce.

Kodayake, wannan ba sabon abu ba ne a jihar a cewar wani mazaunin garin kasancewar masallatai daban-daban na karɓar kuɗi kama daga Naira 10,000 zuwa 30,000.

Sai dai rahoton da aka samu dangane da kuɗin da Masallacin Lekki ya karɓa a wannan shekara ya zarce na kowa a jihar, lamarin da ya ja hankalny jama’a a ciki da wajen jihar.

Continue Reading

Addini

Yadda azumin Ramadan ke taimakawa wajen tunatarwa da ƙara kusanci da Allah da kuma iyali

Published

on

Watan tara na Hijira a kalandar Musulunci wanda asalinsa ke nuna tarihin yadda Annabi Muhammad (S.W.A) ya yi ƙaura daga Makka zuwa Madina, a lokacin ne al’ummar Musulmai sama da biliyan 2.5 a faɗin duniya suke azumi a watan Ramadan.

Ana gudanar da azumin ne har tsawon ranakun watan baki daya tun daga ketowar alfijir zuwa faduwar rana tare da addu’o’i da kuma tunatarwa Kamar yadda koyarwar Annabi (S.A.A.W) ya bayyana.

Watan Ramadan ba wai kawai yana ƙara wa muminai ayyukan ibada da kuma tunarwa ba ne, falalal cikin wata mai alfarma yana ciyar da gangan jiki da tunani gwargwadon yadda yake tsarkake ruhi.

Lokaci ne na musamman na kamewa da kuma yin ibada da mubaya’a da ya hada biki na ibada da kuma iyali, da al’umma a lokaci guda.

Azumin Watan Ramadan

A cewar Alƙur’ani mai tsarki, azumi wani nau’i ne na ibada da aka wajabtawa dukkan muminai.

“Ya ku waɗanda kuka yi imani, an wajabta azumi a kanku, kamar yadda aka wajabta wa waɗanda suka gabace ku, saboda ku zama tsarkarku,” a cewar wata aya daga Suratul al-Baqarah a cikin Alƙur’ani.

A cewar malaman addinin Musulunci, azumi wajibi ne a watan Ramadan kuma yana da fa’idodi da falala masu yawa ga kowane mutum.

”Wannan ne watan da mutane za su nemi gafarar Allah a kan kurakuran da suka aikata, sannan suna amfani da wannan damar wajen kyautatawa iyalansu da abokansu da kuma al’ummar da suke rayuwa a cikinta,” kamar yadda malamin addinin Islama da ke Nairobi Sheikh Shaaban Ismail ya shaida wa TRT Hausa

“Duk musulmin da ya kai shekarun balaga ko sama da haka, ban da wasu ƴan tsiraru, wajibi ne su yi azumi.”

Shika-shikan Musulunci

Azumin watan Ramadan na ɗaya daga shika-shikan Musulunci guda biyar, waɗanda wajibi ne ga dukkan Musulmai su yi riƙo da su.

Na farko shi ne “shahada”, ko kuma kalmar imani da cewa Allah shi ne abin bautawa shi kadai, kuma Annabi Muhammadu manzonsa ne.

Na biyu shi ne tsayar da salloli biyar a rana sai kuma Azumi a watan Ramadan da bayar da “zakka” (aikin ba da sadaka), da kuma ziyarar Makka don yin aikin Hajjin ga wadanda suke da halin zuwa.

Iyaye Musulmai gaba ɗaya sukan koyar da ƴaƴansu tun suna ƙanana ɗaukar azumin watan Ramadan a matsayin umarni daga Ubangiji, da nufin amfanar da su ta hanyar wadatar da kowane fanni na rayuwarsu.

“Wasu daga cikin wadanda azumin bai wajaba a kansu ba sune tsoffi da marasa karfi da suka hada da masu fama da lalurar ajali, a maimakon haka ana bukatar su ciyar da miskini abinci duk ranar wata,” in ji Sheikh Shaaban.

“Idan mutum yana fama da wata rashin lafiya na ɗan wani lokaci ko kuma ya kasance matafiyi ko kuma mai ciki ko mai shayarwa, ko mai jinin haila, an kebe masu irin wannan lalura daga yin azumi, tare da gargadi kan cewa sai mutum ya rama ta hanyar sake yin azumin daga baya”.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe gomman Falasɗinawa a ranar farko ta Azumin Ramadana

Faɗaɗa ayyuka

Azumin Ramadan ba wai kawai kaurace wa ci da sha ba ne. Dole muminai su ƙaurace wa sha’awarsu kamar yin jima’i. Ana kuma buƙatar musulmi su kara taimakawa marasa karfi a cikin watan.

A bayyane yake cewa a tsawon shekaru har wasu da ba musulmai ba sun yarda tare da shaida muhimmancin watan Ramadan.

A faɗin duniya baki ɗaya, wasu waɗanda ba musulmi ba su kan yi azumi a cikin watan Ramadana mai tsarki- wasu don samun biyan bukatu na ruhinsu da kuma keɓe kawunansu don tarbiyyar da ke tattare da watan, wasu kuma don su ji yanayin da ake ji, wasu kuma a matsayin sadaukarwa ga mutanen da ke kusa da su.

“Ana so Musulmai su nisanci duk wani aiki na zunubi ko kuma na rashin ɗa’a a kowane lokaci, sannan a cikin wannan wata ana bukatar su faɗaɗa ayyukansu na alkhairi da kuma gujewa duk wata shagala ko wacce iri ce.

“Idan aka kiyaye, hakan zai kawo zaman lafiya da wadata a cikin al’umma gaba daya,” a cewar Sheikh Shaaban.

Al’adar buda Iftar, ko buɗa baki bayan faɗuwar rana a kowace rana, wani ɓangare ne na watan Ramadan wanda ya zarce iya addini kawai.

A mafi yawan lokuta, mutane kan gayyaci ’yan uwa da makwabta da abokan arziki domin su buda baki tare ta hanyar cin nau’in abinci irin daban-daban gami har ma wasu na musamman da ake ci a lokacin Ramadan.

Don haka, lokacin buɗa baki ba wai dabi’a ce ta buɗa baki kawai ba, hanya ce ta haɗa kai da kuma ƙara ɗankon soyayya da kautatawa a tsakanin al’umma.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like