Dawakin Tofa, Tofa Da Rimin Gado Canji Ya Zo?

0
292

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

Babu shakka, kananan hukumomin Dawakin Tofa da Rimin Gado da Kuma Tofa  sun kasance mazaba ta tarayya wadda Kuma ta sami wakilai da suka gudanar da wakilci gwargwadon iyawar su, tun lokacin da Nijeriya ta koma Kan hanyar dimokuradiyya a shekara ta 1999. 

Haka Kuma mutanen wannan mazaba sun kasance masu matukar son zaman lafiya da kwanciyar hankali da Kuma bin dokokin kasa wanda hakan ta sanya a tarihi irin na siyasar wannan zamani ba’a taba samun wani rikici kan wani shugaba ba duk da yadda ake samun mabanbantan ra’ayoyi.

A wannan tsokaci da na fara, zan bayyana yadda wannan mazaba Mai kananan hukumomi guda uku masu Albarka watau Dawakin Tofa da Rimin Gado da kuma Tofa suke da ra’ayin samun chanjin wakilci a majalisar tarayya a zabukan shekara ta 2023 idan Ubangiji ya nuna mana.

Duk da cewa wakilan da suka wakilci wannan mazaba sunyi kokari sosai wajen kawo abubuwa na  ci gaban yankin, sai dai mafiya yawan mutanen dake mazabar sun bayyana cewa yana dakyau  su Sami sabon wakili a majalisar wakilai domin shima ya jarrabawa nasa kokarin duba da cewa kowane dan kasa Yana da damar ya tsaya takara ko Kuma ya zabi shugaba.

Leave a Reply