Yadda Na Ji Da Aka Kashe ‘Yata Mai Ciki A Gidanta Da Ke Jigawa

0
529

Daga; Rabo Haladu.

Mutane na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan rahoton mutuwar Ummi Garba, wata matar aure mai ciki da aka kashe a gidanta da ke ƙaramar hukumar Haɗeja a jihar Jigawa.

Masu amfani da kafafen sa da zumunta sun nuna kaɗuwa da takaicin wannan kisa da aka yi wa matar auren.

Mahaifinta da ake kira Malam Garba Umar ya shaida cewa wasu mutane ne suka shiga gidanta suka kashe ta.

A tattaunawar tasa da manema labarai, mahaifin Ummi ya ce ganin da ya mata na ƙarshe shi ne a ranar Lahadi lokacin da ta je bikin ƙanwarta gida.

Ummi ta zo gida a ranar Lahadi kuma tare muka wuni saboda ana bikin ƴar uwarta, kafin daga bisani mijinta ya zo ya ɗauke ta suka tafi, shi ne ganin da ya yi wa ƴar tasa na ƙarshe.”

“Ɗan uwana ne ya kira ni a waya ranar Laraba ya shaida mini cewa wasu mutane sun kashe Ummi, nan da nan na tafi gidanta, abin da idona ya gani na takaici ne kuma ba zan taɓa mantawa da hakan ba.”

Malam Garba ya ce a kan idonsa aka fitar da gawar Ummi a gidan da take zaune da mijin da ta aura wata 19 da suka gabata.

Ya tabbatar da cewa ‘yar tasa na ɗauke da ciki kamar yadda ma’abota shafukan sa da zumunta ke ta faɗa a shafukansu.

“Eh tana da juna biyu kuma tana zuwa awo, cikin shi ne na biyu bayan na farkon da ta samu wanda aka yi barin shi bayan wani lokaci.”

Ya ce ƴar tasa mai shekara 26 tana da biyayya kuma ba zai taba mantawa da ita ba.

A ƙarshe ya yi fatan cewa hukumomi za su yi abin da ya dace wajen gano wadanda suka yi wa ‘yar tasa kisan gilla.

A gefe daya, ‘yan sanda sun tabbatar da kisan matar, tare da cewa mijinta Mu’azu Babangida na asibiti yana karɓar magani.

A cewar kakakin ‘yan sandan Jihar Jigawa, DPS Lawal Adam, sun samu rahoton faruwar lamarin ne da misalin karfe 6:15 kan abin da ya faru, kuma da zuwan su suka tarar da Ummi cikin jini an kuma yanka wuyanta.

Ya ce “wani abu mai kaifi suka yi amfani da shi suka yanka wuyanta, lokacin da jami’anmu suka je wurin ta riga ta rasu.”

“Mijinta ya dawo daga aiki ya tarar da ita jina-jina a kwance, a yanzu da muke magana yana asibiti yana karɓar magani.”

Mutanen Hadeja dai sun ta nuna bacin ransu a Facebook kan wannan kisa da aka yi wa Ummi, kuma suna kira ga hukumomi su dauki matakin da ya dace cikin gaggawa.

Yusuf Muhammad Nadabo wanda ya wallafa hoton marigayoyar ya ce yana da mahimmaci hukumomi su mayar da hankali kan bankado wadanda suka yi aikin, ko dan zuciyar mutanen garin ta huce.

Hakazalika, a watan Fabrairun 2022, wasu mutane sun shiga gidan wata mata Rukayya Mustapha a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya suka kashe ta.

Matar da ke zaune a unguwar Danbare ta mutu ne sakamakon dukan da aka yi mata in ji ‘yan sanda kuma an yi wa yayanta duka suma.

A watan Afrilun 2022, wani mutum da ake zargi shi ma ya kashe matarsa da ake kira Mercy Samuel a Jos a arewacin kasar, shi ma ya ja hankali.

.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here