El-Rufa’i Ya Yaba Wa Kamfanin Brewery Ta Najeriya Bisa Gina Ofishin ‘Yan Sanda A Kudenda

0
294

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

GWAMNAN Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i ya yaba wa kamfanin samar da giya ta Najeriya, wato (Nigerian Breweries, NB Plc) bisa gudummawar samar da ginin ofishin ‘yan sanda a Kudenda, ta Jihar Kaduna.

Kafin kaddamar da ginin ofishin, ‘yan sandan tun a shekarar 1997 sun yi hayar gida mai dakuna biyu don amfani da su a matsayin ofishin su.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin kwamishinan kirkire-kirkire na kasuwanci, Farfesa Kabir Mato ya bayyana cewa kamfanin a tsawon shekaru yana ci gaba da dawo da ribar da yake samu ga al’umma ta hanyar Cooperate Social Responsibility, (CSR) maimakon raba dukkan ribar ga masu hannun jarin.

Ya kuma godewa kamfanin bisa yadda ta ke kokarin karawa Gwamnatin kaimi ta hanyar tallafawa a wasu kadan daga cikin ayyukan da ya rataya a wuyanta, ya kuma kara da cewa al’umma za su ci gaba da nuna godiya da irin kokarin da kamfanoni giyar Najeriya ta ke yi.

Mato ya kuma yabawa kamfanin kan kayayyakin tallafi da aka raba wa mata da matasa a lokacin horon koyon sana’o’i da aka yi a Kaduna kwanan nan.

Don haka Kwamishinan ya bukaci sauran ‘yan kasuwa da ke Kaduna da su yi koyi da halayen Kamfanin na Nigerian Breweries Plc, musamman a tsarin ta na (CSR).

A nasa jawabin, kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kaduna, CP Yekini Ayoku, ya ce kamfanin giyan na Najeriya ya maye gurbin gidan da aka yi hayar a matsayin ofishin ‘yan sanda tun 1997 da wani katafaren gini mai kyau domin inganta tsaro a tsakanin al’umma.

CP ya kuma bukaci sauran kamfanoni da su yi koyi da matakin da Kamfanin Breweries plc ta dauka na karbar bakuncin al’umma, yana mai jaddada cewa hakan zai taimaka matuka wajen rage aikata miyagun laifuka a cikin al’umma.

Sai dai ya yi gargadin cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya ba za ta amince da duk wani nau’i na kai hari a cibiyar ko jami’anta ba, yana mai bayar da tabbacin cewa za a samar wa Ofishin da dukkan kayayyakin da ake bukata.

Tun da farko, Manajan harkokin kamfanoni na yankin Arewa, Mista Kabiru Kassim ya yabawa gwamnatin Jihar Kaduna bisa samar da yanayin da zai taimaka musu wajen gudanar da harkokinsu.

Ya ce a matsayinsu na ‘yan kasuwa sun samu kyakkyawar alaka da jama’ar jihar Kaduna tsawon shekaru 59 da suka gabata, kuma a kwanan baya an ba su lambar yabo mafi kyawun kungiyar masu biyan haraji.

“A kokarinmu na tallafawa gwamnatin jihar Kaduna mun bullo da wasannin makarantar Maltina, kacici-kacici na watan Ramadan da lambar yabo ta Malama Maltina da dai sauransu”.

Shima da yake magana, Manajan Kamfanin Kudenda, Mista Olusoji Onigbinde, ya ce, kamfanonin Breweries na Najeriya sun dau tsawon wannan lokaci sakamakon tallafin da suke samu daga al’ummomin da suka dauki nauyinsu.

“Don haka ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen bayar da goyon bayanmu, musamman ga gwamnatin jihar Kaduna da hukumominta idan bukatar hakan ta taso.”

“Daga cikin alhakin ayyukanmu na jihar Kaduna ya hada da, tallafawa gwamnati ta hanyar bayar da gudummawar zunzurutun kudi naira miliyan 20 a matsayin asusun shiga tsakani na COVID 19, bayar da gudummawar hadarin da ya faru da gaggawa a asibitin Gwamna Awan, Kakuri da kuma VVF ward a Gambo SawabaAsibiti, Zaria da sauransu”.

Bikin ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da sarakunan gargajiya da sauran al’umma.

Leave a Reply