Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’addan Boko Haram Sama Da 10, Sun Kama Manyan Motoci Guda 3 A Borno

0
283

Daga; Sani Gazas Chinade, Maiduguri.

KWAMANDAN Dakarun sojan Operation Hadin Kai (OPHK), Maj-Gen. Christopher Musa, ya ce an kashe ‘yan ta’addan Boko Haram sama da goma a yankin Lawan Minari, karamar hukumar Konduga da ke kan titin Maiduguri/Damaturu a Jihar Borno.

A cewarsa, an kuma kama manyan Motoci masu dauke da bindigogi guda uku, bayan da ‘yan ta’addan suka kona manyan motoci biyu da wata tankar mai a kauyen.

Musa ya bayyana hakan jiya a Maiduguri ne, cewa ‘yan ta’addan sun tashi ne daga dajin Sambisa domin tsallakawa dajin Sasawa a Jihar Yobe.

“Dakarun kasa sun bi su a kan titi da cikin daji, yayin da jirgin yakin Tucano ke kokarin lalata motocin, kafin su kashe wasu daga cikin ‘yan ta’adda,” in ji shi.

Ya kara da cewa wasu daga cikin ‘yan ta’addan sun tsere da harbin bindiga zuwa dajin Yobe.

Jaridar GTK ta samu labarin cewa tun farko ‘yan ta’addan sun yi wa masu ababen hawa da matafiya kwanton bauna a kan hanyar.

Leave a Reply