Yadda ake yin Miyar Yalo/Ɗata

0
586

Daga Fatima MONJA, Abuja

Shin Matan gida bamu gaji ya kaiwa markeɗe ko jiran wuta ba? gwada wannan miyar kici shi da shinkafa ko Doya.

MIYAR YALO

ABUBUWAN BUƘATA

Yalo
Attarugu
Tattase
Albasa
Kifi Sukunbiyya
Crayfish
Citta
Tafarnuwa
Tumatir(in kina so)
Manja
Sinadarin ɗandano
Kori

Yalo

Yadda zaa hada

Da farko zaki samu Yalon ki mai kyau, ki wanke da gishi sai kisa a ruwa kaɗan a ɗora akan wuta, yayi kaman minti taƙwas zuwa goma, sai a sauke a tace ruwan a barshi ya huce sannan a jajjaga shi.

Sai a wanke kifi sosai a tafasa da gishiri ko a gasa yadda yafi ma Uwargida sauƙi, sai a gyara a cire kayan cikin. Uwargida sai ki yanka albasan ki isashshe ki jajjaga Citta da tafaruwa, sannan attarugu, da tattase.

Sai uwargida ta ɗora tukunyan tasa manja in yai zafi sai a ɗauki albasa a zuba yayi kaman minti 1 sai a zuba citta da tafarnuwa a juya, sai a deɓo jajjagen attarugu a zuba a sa sinadarin ɗandano, sai a bari ya soyu kafin a kawo jajjagen yalo, kifi da crayfish zuba a juya a hankali, sai a sa ɗan kori in ya yayi kamaan minti 2 sai a sauke shi.

Ana cinta da farar shinkafa, doya, da sauransu.

Leave a Reply