Miyar ganyen alayyahu (eforiro)

0
340

Daga Fatima MONJA, Abuja

Abubuwan buƙata

kayan miya
nama sa, ko na kaza
crayfish
stockfish
Kayan ciki
manja
alaiyahu
Dunƙulen ɗanɗano
Kayan ƙamshi

YADDA ZAAYI

Ki sami stockfish ki wanke ki jika a aje gefe. Ki tafasa kayan ciki da nama, kisa albasa da tafarnuwa, da dunkulen dandano da kayan ƙamshi. Sai a yayyanka tattasan, albasa, tumatir a tsaitsaye. A ɗora manja a wuta kaɗan, se a zuba kayan miyar a soya, a zuba crayfish dakakke, da naman da kika dafa da stock fish din kisa ɗanɗano da kayan ƙamshi, ki rufe sai komai ya dahu. Dama tuni kin wanke alaihun ki ba tare da kin yanka ba, sai ki dan sa ruwa ruwan zafi akansa ki wanke dan yi laushi, daganan se ki haɗa cikin miyar ki juya. Ba a so allayyahun ya wuce minti biyu a wuta tunda an riga an wanke da ruwan zafi.

Zaki iya ci da shinkafa, sakwara, ko tuwo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here