Connect with us

Bidiyo

Alalar Dankali

Published

on

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Bidiyo

Duk wani juyin mulki idan ya samu awa 24, to ya zaunu – Dakta Hassan Gimba a hirarsa da RFI Hausa

Published

on

Daga Ibraheem El-Tafseer

Duk wani juyin mulki, idan ya samu awa 24, to ya zaunu. Wannan kalami ya fito ne daga bakin fitaccen ɗan jaridar nan kuma marubuci, mawallafin jaridar Neptune Prime, Dakta Hassan Gimba, a hirarsa da RFI Hausa ranar Litinin, kan juyin mulkin Jamhuriyar Nijar.

Ya ci gaba da cewa “mutanen da sun yi naɗe-naɗe, sun kawo wani daga Bankin raya Afirka ya zo musu (prime minister), sun naɗa wannan, sun naɗa wancan, ai gwamnati ta riga ta zauna. Tun farkon fari ba a bi abun yadda yakamata a bi ba, kamar yadda Bahaushe yake cewa “an yi sake ɗan Zaki ya girma” yanzu sai dai a lallaɓa su, a samu zaman lafiya”.

Tambaya: An tura ƙungiyar yammacin Afirka domin zaman lafiya, amma suna ta furta waɗansu irin kalamai?

Ai dole su furta kalamai, domin gwamnatinsu ta riga ta zauna, gwamnati ne yanzu mai ci. Kawai dai a san yadda za’a yi a dawo da harkoki kamar na kullum, idan ba haka ba, aka ce za’a ci gaba da takunkumi, sai dai ‘yan ƙasa ɗin su wahala, manyan gwamnati ba zai shafe su ba.

NEMA ta ba da tallafin kayan agaji ga mutane dubu 23 a Nijar

Tambaya: Majalisar Ɗinkin Duniya ECOWAS suna ƙira sojojin, domin a samu maslaha, ba ka ganin suna da kyakkyawar manufa ga Nijar?

Babu wanda zai ce babu kyakkyawar manufa, amma kuma ‘yan ƙasar ne suka ce ga abin da suke so. A lallaɓa ka da jama’a su wahala, ka da bayin Allah su tagayyara.

KU KALLI BIDIYON ANAN

Cikakken bidiyon hirar Dakta Hassan Gimba da RTF Hausa

Tambaya: A halin da ake ciki na sulhunta wa, shi kuma jagoran Sojojin Nijar, ya ma fara batun tsara gwamnatin riƙon ƙwarya, waɗanda za su shafe shekaru uku kan karagar mulki. Shekaru uku a mulkin Soja?

Shekaru uku a mulkin soja ai kamar kwana uku ne. A nan Afirka ba mu ga gwamnatocin Soja inda suka yi shekaru ba? Ko a su ECOWAS akwai waɗanda sun yi shekaru 20, wasu ma 30. Su me za ka ce musu? Sai dai fa a lallaɓa indai ba yaƙi za’a yi ba.

Tambaya: Ka ambaci kalmar yaƙi, wanda Ecowas ta ce ana kan tsara shi?

To shi yaƙi kamar tafiya ne, kai ne da shi, amma ba ka san ƙarshensa ba, haka yaƙi yake. Idan ka fara shi, ba ka san yadda zai ƙare ba. Yanzu alal misali Najeriya, idan ta ce za ta yi yaƙi. Mu kuma fa muna fama da matsalar rashin tsaro. Idan muka buɗe kafa na yaƙi, waɗanda a kudu da suke neman ɓantarewa, Arewa maso gabas da su ma suke neman ɓantarewa, wai su ma suna jihadi. Arewa maso yamma, ana ta fama da masu garkuwa da mutane, su ma kansu ‘yan Boko Haram ne, suna neman ɓantarewa. To da wanne za mu ji?

Idan muka mayar da hankalinmu wai muna yaƙi, shikenan an bar baya da ƙura. Kamar kana tafiya ne, wuta tana cinye ka ta baya.

Tambaya: Idan ana buƙatar dawo da tsarin Dimokraɗiyya a Nijar, ba tare da an kai ruwa rana ba, yaya za’a yi?

Sai a tafi da su waɗannan mutanen gwamnatin, waɗanda yanzu suke kai.

Continue Reading

Bidiyo

Bana son nayi kwantai, zan dinga biyan duk wanda ya aureni albashi inji bududurwa mai neman miji

Published

on

Wata budurwa ‘yar Najeriya da ke rayuwa a ƙasar Faransa ta bayyana halin matsin da take ciki na rashin samun abokin rayuwa.

Ta yi iƙirarin cewa ta mallaki kadarori masu yawa a Najeriya da Faransa, sannan abu ɗaya kawai da ta rasa a rayuwar ta shine abokin rayuwa.

KU KALLI BIDIYON ANAN: https://youtube.com/shorts/PHxLbonPaew?feature=share

A wani bidiyo da ya yaɗu a kafafan sadarwa na soshiyal midiya, budurwar wacce shekarun ta sun fara ja ta bayyana cewa tana ta tsufa gashi har yanzu ta kasa samun abokin rayuwa.

Ta bayyana cewa kuɗi ba matsalar ta bane, sannan a shirye take ta rinƙa bayar da albashi mai tsoka ga duk saurayin da ya yarda ya aure ta.Budurwar har durƙusar da guiwoyin ta tayi ƙasa a cikin ruwan sama tana roƙon samari da su jaraba sa’ar su wajen neman soyayyar ta.

Continue Reading

Al'ajabi

Yadda uba ya kori ɗansa don ya ziyarci mahaifiyarsa

Published

on

Wata mace da ke zaune a ƙaramar hukumar Zariya a jihar Kaduna, Hindatu Haruna ta ce tsohon mijinta ya kori ɗanta ne saboda yawan ziyarar da ya ke kai mata.

Hakan na ƙunshe ne a wani rubutu da wata ‘yar gwagwarmaya a shafukan sada zumunta, Fauziyya D. Sulaiman ta wallafa a Facebook, inda tace Aliyu Nuhu wanda aka kora yaro ne ɗan shekara 17.

A zantawarta da ‘yan jarida ta wayar tarho, mahaifiyar cikin ruɗani ta bayyana cewa mahaifinsa ya kore shi ne bayan ya samu labarin cewa yana zuwa gidanta.

KU KALLI BIDIYON ANAN: https://youtu.be/B_lYSZ5RcBw

“Na ji cewa bayan Aliyu ya dawo gida, mahaifinsa ya tambaye shi daga ina yake? Aliyu yace ya ziyarceni, sai mahaifinsa ya fusata ya ce ya tattara kayansa ya koma gurina.

Aliyu ya san ni na auri wani kuma ba zai iya zuwa ya zauna da ni ba,” in ji ta.

KU KUMA KARANTA:Yadda mace ta yanke azzakarin mijinta, ta kashe shi har lahira

Ta kuma ce ɗanta ya bar gida a watan Disamban 2022 amma babu wanda ya sanar da ita.

Ta ƙara da cewa ” Sai makon da ya gabata na sami labarin, kuma tun lokacin ban yi barci ba.”

Ta yi kira ga jama’a da su taimaka mata wajen neman ɗanta da ya ɓace, inda ta ce duk wanda ya san inda yake to ya kai rahoto ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko kuma wajen wani basaraken gargajiya a Zariya.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like