‘Yan Sanda sunkama matashin daya tsaya akan kabari yana ashar a jihar kano

0
353

Daga Shafa’atu Dauda Kano.

Rundunar Yan sanda a Jihar Kano ta kama matashin nan da ya raba ƙafa akan kabarin wata mata yana surfawa wata dattijuwa zagi sabida sunyi faɗa da ‘yar data haifa kuma yana dauka a bidiyo.

A yau Lahadi ne a ka tashi da ganin wani faifan bidiyo a kafafen sadarwa na wani matashi da ya raba ƙafarsa kan wani kabari ya na ta surfa ashariya a waya, ya na kuma dauka a bidiyo.

Sai dai kuma tuni Abdullahi Ƴar-dubu ya shiga hannun ƴan sandan Caji-ofis ɗin Sharada, inda yanzu haka an tusa keyar sa zuwa shalkwatar ƴan sanda da ke Bompai.

Kakakin rundunar ƴan sanda ta Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da kama matashin, inda ya ce, tuni Mukaddashin Kwamishinan Ƴan Sanda, DCP Abubakar Zubairu ya bawa DPO na Sharada, SP Abdulrahim Adamu umarnin a kamo wannan matashi.

Ya ƙara da cewa yanzu haka an kamoshi kuma an miƙashi babbar shelkwatar rundunar yan sanda da ke bompai.

SP Kiyawa ya ce nan gaba kaɗan za a sanar wa da al’umma halin da a ke ciki.

Tuni dai al’umma su ka fara shi wa rundunar ƴan sandan albarka bisa tashi tsaye da tayi wajen kamo wannan matashin cikin ƙanƙanin lokaci, inda kuma su ka riƙa yi masa tofin alla-tsine.

Leave a Reply