Ya Kamata Ace Mun Yi Tsari Mai Kyau Da Zai Taimaki Kasa A Fannin Noma – Hon Munnir Babba

0
269

Daga; Bashir Bello, Majalisa Abuja.

A YAYINDA kowani fanni ke daukar tsari na fasali mai nagarta a fadin Tarayyar Najeriya wanda hakan ke da nasaba da kawo cigaban harkoki, Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar karamar hukumar Kunbotso, Honarabul Munnir Babba Dan Agundi, kuma shugaban kwamitin kula da cibiyoyin da jami’o’in da kwalejin makarantu na Noma, ya bayyana cewa wajibi ne ayi tsari na musamman wanda zai taimaka wa fannin Noma a kasar.

Dan Majalisar Honarabul Munnir, wanda ya bayyana hakan a yayin zantawa da manema labarai, ya bayyana cewa Dokar da aka gyara a ma’aikatar mai kula da aikin binciken Noma da makarantun na Tarayya, ya biyo bayan yadda wadannan cibiyoyin ko ma’aikatun suke gudanar da harkokinsu tamkar yadda wasu kasashe kamar Indiya da Burazil suka bunkasa.

Ya kara da cewa a bisa Dokar da aka tsara wacce take ta hukumar bincike ta harkar Noma (ARCN) kuma ake dubawa don yin gyara ta yadda zai zama cewa duk wasu kwalejin makarantun Noma suna karkashin wata hukuma, wanda hakan zai sa a samu damar gudanar duk wasu harkoki ta yadda ya dace ba tare da an samu wata matsala ba domin wannan Dokar ta ARCN, za ta kawo gyare-gyaren da ake bukata.

Acewarsa, wasu daga cikin wadannan makarantun na da cibiyoyin bincike, hadi da wasu mambobin da suke tafiyar da harkokin bincikin amma a kan samu matsaloli wajen gudanar da harkokin sakamakon wasu yan siyasa ke yin katsalandan a cikin al’amuran, wanda harkar bincike irin wannan tana da bukatar mutane wadanda suke da kwarewa da dabaru da za suyi a fannin.

Ya ce “saboda irin wannan gyare-gyaren ne yasa muka ga cewa ya kamata ayi hakan domin sauran kasashen da muka je muka koyo aikin tare dasu duk suna ci gaba kuma duk sun fi mu bunkasa a harkar Noma bayan duk mun fara tare dasu ne, toh amma yanzu alhamdullah domin ta hanyar yin gyare-gyaren muna saran za a samu nasara wannan karon.”

“Kuskuren da aka samu wanda yake da bukatar gyara a yanzu dukda yake an sa hannu a takardar Dokar ita ce an turawa shugaban kasa takardar da suna cewa za a Kafa Makarantar a karkashin ma’aikatar Ilimi amadadin ma’aikatar Noma, toh kuma an gyara har shugaban Kasar yasa hannu domin tabbatar da an Kafa Makarantar ta zauna da gindin ta.”

“Toh wannan magana ce ta gyara kawai don haka ba wata matsala bace domin ina ganin abu ne na Ilimi kuma ana da bukatar mutane su samu ilimin domin cigaban kasa saboda sai da Ilimi zaiyu tunda idan ba Ilimi, babu ta yadda za ayi aci gajiyar tafiyar illa kawai muna bata lokacinmu ne.”

Shugaban Kwamitin ya ci gaba da cewa a Dokar da aka turo wacce zata sama wa cibiyoyin binciken hanyar samun Kudi kamar na TETFUND, wani abu ne wanda yake tsari mai Kyau domin kara inganta sashen harkar Noman domin tabbatar da wani tsari wacce zata rika tallafawa da kudaden da za a rika yin bincike saboda a yanzu basu da wani tsari wanda zaizo sai dai daga asusun Gwamnatin Tarayyar.

Da yake tsokaci kan batun gurbataccen man fetur wanda Majalisar ta bada matsayin ta a kai, Honarabul Munnir ya yaba da irin Matakan da majalisar ta dauka na ganin cewa an kawo Karshen samun matsaloli irin wannan ya Allah koda bisa kuskure, ko sakaci ko son rai ne ya haifar da wannan damuwar wacce ta ke addabar al’ummar Kasar a halin yanzu.

Leave a Reply