Wasu Mahara Sun Hallaka Sama Da Mutum 100 A Kanam Ta Filato

0
469

Daga; Isah Ahmed, Jos.

WASU gungun mahara da ba a gane ko su waye ba, kan babura sama da guda 70, dauke da bindigogi sun kai hari, a wasu kauyuka a Karamar Hukumar Kanam da ke Jihar Filato, a safiyar ranar Lahadi a inda suka kashe sama da mutum 100 da kona gidaje sama da 100 da sace shanu masu tarin yawa.

Wasu ganau sun shedawa wakilinmu cewa, maharan sun kai harin ne a kauyukan Kukawa da Gyanbahu da Dungur da ke Karamar Hukumar Kanam da misalin karfe 11 na safiyar ranar Lahadi a inda suka kashe mutane da dama tare kona gidaje sama da 100 da sace shanu da dama.

An yi jana’izar sama da mutum 100, da aka gano gawarwakinsu a wadannan kauyuka, a ranar Litinin, kwana daya bayan kawo harin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Filato, ASP Ubar Gabriel ya bayyana cewa tuni rundunar su, ta tura jami’anta zuwa yanki amma bai fadi yawan adadin mutane da dukiyoyin da aka rasa ba.

To amma Shugaban Karamar Hukumar ta Kanam, Alhaji Dayyabu Yusuf Garga ya tabbatarwa da ‘yan jarida cewa, a kalla an kashe sama da mutum 100 a wannnan hari da aka kai.

“Ni da kaina tare da sauran jama’a mun ziyarci kauyukan da aka kai wannan hari. Kuma mun yi jana’izar sama da mutum 100, da aka kashe a wannan hari. Amma tuni an tura jami’an tsaro zuwa yankin don ganin an dawo da doka da oda”.

Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya baiwa jami’an tsaro umarnin, su kamo maharan da suka kawo harin. Don ganin an hukumtasu kan wannan mummunan aika aika da suka aikata. Gwamnan ya bada wannan umarnin ne, a cikin wata sanarwa da Daraktan watsa labaran gwamnan, Dokta Makut Simon ya fitar.

Gwamnan ya yi nuna takaici tare da Allah wadai da wadannan hare hare da aka kai. Don haka ya bada tabbacin kamo wadannan mahara domin su fuskanci hukumci.

Jihar Filato dai, ta sha fama da rikice-rikice da ke da nasaba da kabilanci da addini, amma a baya-bayan nan ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, sun ta’azzara matsalar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here