Har Yanzu Dokta Jamil Gwamna Ne Shugaban KEDCO – Inji Ibrahim Shawai

0
322

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

MATAIMAKI na musamman ga shugaban kamfanin samar da wutar lantarki (KEDCO) Dokta Jamil Isyaku Gwamna kan kafafen yada labarai watau Ibrahim Sani Shawai ya sanar da cewa har yanzu Jamil Gwamna ne shugaban wannan kamfani sabanin yadda wasu kafafen labarai suka wallafa cewa an sauke shi daga kan wannan mukami nasa.

A cikin wata sanarwa da Ibrahim Sani Shawai ya fitar ya bayyana cewa ” har yanzu Dokta Jamil Gwamna shi ne shugaban kamfanin na KEDCO kuma batun da wasu jaridu suka wallafa cewa an sauke shi daga wannan matsayi ba gaskiya bane illa yunkurin bata masa kyawawan nasarorin da yake samu a shirin sa na shiga takarar gwamna a Jihar Gombe a zaben shekara ta 2023″.

Sanarwar ta kara da cewa maganar da wadancan jaridu suka wallafa na batun korar Dokta Jamil Gwamna babu kanshin gaskiya a cikin ta, sannan tace shugaban kamfanin na KEDCO mutum ne mai tsari da bin dokokin kasa, don haka nan gaba kadan zai ajiye wannan matsayi nasa domin tsunduma cikin harkokin siyasa bisa sharuddan shiga zabe.

Haka kuma sanarwar ta gargadi kafafen labarai da suka buga wannan labari na cewa an salami Dokta Jamil Gwamna da su gaggauta fitowa fili su baiwa shugaban hakuri tare da janye wannan rahoto da suka bayar domin kaucewa daukar mataki na shari’a kansu.

Malam Ibrahim Sani Shawai ya yi amfani da wannan dama wajen yin Kira ga al’umma da su sani cewa har yanzu Dokta Jamil Gwamna shi ne shugaban kamfanin na KEDCO kuma labarai da aka wallafa cewa an sallame shi kan wasu zarge-zarge na almundahana da dukiyar hukumar ba gaskiya bane.

Leave a Reply