Zaben 2023: A Daina Yiwa Shugabannin PDP Na Kaduna Ta Arewa Zagon Kasa – Dattijo

0
516

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

SHUGABAN Kungiyar Kamfen din Samaila Suleiman, Honarabul Adamu Dattijo ya yi kira ga tsohon dan Majalisar Wakilai na Tarayyar Najeriya da masu kula da kafafen sadarwar zamani din shi da su daina yi wa Dattawa da jami’an PDP zagon kasa a Kaduna ta Arewa gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Dattijo ya bayyana cewa kungiyar Kamfen dinsa na sane da zargin da Dan takarar da masu rike da mukamansa ke yi na cewa ana amfani da wasu kudade ga jami’an jam’iyyar don siyan ra’ayin wakilan jam’iyyar don yin mubayi’a gare shi gabanin zaben fidda gwani, inda ya dage kan cewa wani dan takara ba zai iya siyan jami’an PDP ba, haka ma ba za su iya siyan jam’iyyar ba.

Ya ce “Ina so na karyata maganar bada makudan kudade ga Jami’ai, Kansiloli ko duk wasu masu ruwa da tsaki dake cikin Jam’iyyarmu kamar yadda ake ta yada jita-jita da yin zargi.”

“Mun ga kungiyar ABG Support Group a dandalin sada zumunta na yanar gizo suna fadin munanan kalamai a kan kansilolinmu domin bata sunan mu a gaban jama’a da jajirtattun ‘yan jam’iyyar mu.

“Ya kasance wata dabi’a ce ta Honarabul Samaila Suleiman, inda ya saba ba wasu al’ummar mazabarsa kyaututtuka da kayan abinci a duk lokuta na watan Ramadan, kamar su Malaman Addini, Kungiyoyin Matasa, Kungiyoyin Mata da sauran su ba tare da yin la’akari da wani banbancin akida ba musamman a lokutan bukukuwa kamar na Ramadan, Sallah, Kirsimeti da Easter”

“Saboda haka, kuskure ne kowa ya yi ta zage-zage cewa Hon. Suleiman yana bayar da kudi ga shugabannin PDP na Kaduna ta Arewa da masu goyon bayan jam’iyyar.”

“Idan har za a iya zargin duk wani mai neman tikitin PDP da laifin Zagon Kasa da hadin bakin jam’iyyar APC, to ya kamata wannan tsohon dan majalisar da ya kasance yana samun goyon bayan yan adawa da cikakken goyon baya daga fadar gwamnatin APC ta hannun Hon. Mamman Legas da sauran su, jiga-jigan jam’iyya mai mulki da ke ta neman yin kiraye-kiraye ga jami’an jam’iyyar PDP suna neman su kada kuri’unsu ga wanda ya ce sun yi yunkurin ba su makudan kudade.

“Ya zuwa yanzu dai, wannan dan takarar ya karbi kudi naira miliyan 20 da kuma babura 30 a matsayin gudunmawa daga wajen wani sanata mai ci a jam’iyyar APC ta hanyar Hon. Mamman Legas na jam’iyyar APC wanda muke da shaidun da ba za a iya musantawa ba kuma za a iya tabbatar da su na kiran waya da kuma rikodin sauti.

“Wannan ba lokaci ba ne da za a haifar da rarrabuwar kawuna da haifar da rikici a tsakanin mambobinmu da ya kamata a bar su su mai da hankali kan yadda babbar jam’iyyarmu za ta samu kyakkyawar nasara a zaben 2023.”

“Kyakkyawan misali shi ne abin da ya faru a zaben kananan hukumomi da aka gudanar kwanan nan a Kaduna ta Arewa inda wannan dan takarar da ke son wakiltar Kaduna ta Arewa a Majalisar Wakilai ya yi fatali da damar da PDP za ta samu na samun kujerar shugaban karamar hukuma ta hanyar hada kai da APC.

“Irin wannan mutumin ba shi da wani dalili na ɗabi’a da zai tuhumi wasu da yin zagon ƙasa saboda a halin yanzu burin Jam’iyyar a kananan hukumomi da ya kashe tana binsa,” in ji shi.

Leave a Reply