Malaman Addinin Islama 6 Sun Rasu A Hadarin Mota A Kano

0
364

Daga; Rabo Haladu.

WANI mummunan hadarin mota yayi sanadin mutuwar wasu malaman addinin Islama shida a jihar Kano a ranar Laraba.

Malaman sun rasu ne a kan hanyarsu ta komawa Kano daga karamar hukumar Sumaila bayan sun kammala aikin da’awah a karkashin gidaunyar Imam Malik.

Wata ma’aikaciyar gidauniyar ta shaida cewa da misalin karfe 3 na yammaci suka sami labarin hadarin.

Ta ce hadarin ya rutsa da dukkan malamai shida, wadanda jagororin aikin da’awa ne na gidauniyar.

Sai dai hukumar kiyaye hadurra, FRSC ta ce ba a sanar da ita aukuwar hadarin ba, amma kakakin hukumar ya shaida cewa za su gudanar da bincike.

Leave a Reply