Ramadan 2022: Sheikh Dahiru Bauchi Ya Yi Bude Baki Tare Da Malaman Addinin Kirista A Kaduna

0
450

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

TAWAGAR malaman addinin Kirista daga wasu sassa na Jihohin Arewacin Najeriya 19 a karkashin jagorancin Fasto yohanna buru sun ziyarci gidan Sheikh Dahiru Usman Bauchi dake Kaduna da nufin hada kai da sauran malaman addinin musulunci wajen yin buda baki na Azumin watan Ramadan, kana da neman kara karfafa alaka tsakanin kiristoci da musulmi.

Jagoran tawagar Fasto Yohanna Buru wanda yake Babban mai kula da Cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministry, dake Sabon Tasha, kaduna, sun yi buda bakin ne tare da takwarorinsu musulmai a gidan fitaccen malamin addinin musuluncin ne, Sheikh Dahiru Bauchi a yammacin ranar laraba a gidansa dake garin Kaduna domin kara kyautata alakar dake tsakaninsu.

Yayin da yake jaddada alakarsu wacce ta ke tun shekaru 11 da suka gabata, sun gudanar da yakin neman zaman lafiya a lokacin buda baki domin cudanya da mu’amala da galibin malaman addinin Musulunci na Najeriya, wadanda suka hada da Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad , Sheikh Ibrahim Yakub elzazzaky, Sheikh Dahiru Bauchi, Sheikh Salihu Mai Barota, Sheikh Mohammed ibn Abdul na Jihar Neja, da ma wasu kasashe makwabta na Afirka kamar Jamhuriyar Nijar da Jamhuriyar Benin, da nufin wa’azi da inganta zaman lafiya da hadin kai a lokacin buda baki.

Buru, ya yi nuni da cewa, zuwa yin buda bakin na watan Ramadana na ba da wata dama ga Kiristoci wajen yin cudanya da Musulmi da inganta fahimtar juna a tsakanin mabiya addinan biyu.

Jagoran tawagar kiristocin ya ce taron wanda shi ne karo na 11 kuma an yi shi ne domin inganta dangantakar addinai, tattaunawa, zaman lafiya, hadin kai, yafiya da kuma hakuri da juna tsakanin mabiya addinan Najeriya biyu.

“Muna yin haka ne domin inganta hadin kai a tsakanin addinai da kuma gujewa duk wani nau’in rikicin addini, siyasa da na kabilanci da ke haifar da zaman lafiya a yankin.”

“Mun shafe shekaru da dama muna tafe tare da limaman cocinmu da masu yin bishara da kuma dattawan coci don ganawa da manyan malaman addinin Musulunci domin yin bude bakin azumin watan Ramadanan da neman kara sanar da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin al’umma baki daya.”

A bana Ramadan ya zo ne a cikin tsadar kayan abinci a kasuwanni, kalubalen rashin tsaro da tashe-tashen hankula sakamakon ta’addanci, ‘yan fashi da garkuwa da mutane a yankin, don haka a hada karfi da karfe wajen yin kira ga ‘yan Najeriya da su tashi tsaye wajen addu’ar Allah ya kawo mana dauki da kawo mana karshen rashin zaman lafiya da ya shafi dukkan kasashe.

“Dole ne mu tuna cewa mu iyali ɗaya ne a ƙarƙashin Allah. Dukkanmu muna da littattafai masu tsarki daga Allah ɗaya, mu ‘ya’yan Adamu ne da Hauwa’u, muna da abubuwa da yawa na kamanceceniya da juna.”

Da yake bayani bayan kammala shan ruwan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya nuna farin cikinsa da ziyarar inda ya godewa mabiya addinin kirista daga Jihohin Arewa daban-daban da suke tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a kasar.

Ya kuma jaddada bukatar a kara yin addu’a a kasa domin Najeriya ta shawo kan lamarin da ake ciki.

Yayin da yake kira ga shugabanni da su tuna da ranar shari’a, ya bukaci Musulmi da Kirista da su zauna lafiya da juna a kodayaushe.

Sheikh Dahiru Bauchi ya ce, “amininmu tsohon ministan wasanni Barista Solomon dallung bai samu damar halartar taron na bana ba, amma ya aika da sakon fatan alheri ga daukacin musulmin kasar nan na watan Ramadan 2022.

Leave a Reply