VLADIMIR PUTIN: Gwauro mafi faɗa a ji a duniya

0
512
Gwauro
Vladamir Putin

Vladimir Vladimirovich Putin dan siyasan kasar Rasha ne kuma tsohon jami’in leken asiri wanda shi ne shugaban kasar Rasha, mukamin da ya rike tun a shekarar 2012, kuma a baya daga 2000 zuwa 2008. Ya kuma kasance firayim minista daga 1999 zuwa 2000, da kuma daga 2008 zuwa 2012..

Vladímir Vladímirovich Putin ɗan siyasan Rasha ne. Shi ne shugaban ƙasar Rasha a halin yanzu.

An haifi Putin  a Leningrad, yanzu Saint Petersburg, a ranar Bakwai ga Oktobar, Alif da Ɗari Tara da Hamsin da Biyu (1952). Sunan Mahaifinsa Vladimir Spiridonovich Putin, Sunan Mahaifiyarsa Maria Ivanovna Shelomova. 

Ya kasance Firayim Ministan Rasha daga shekarar Alif da Ɗari Tara, zuwa farkon shekarar Dubu Biyu (1999-2000), sannan ya zama Shugaban Rasha daga watan Maris, shekarar Dubu Biyu, zuwa watan Mayu, na shekarar Dubu Biyu da Takwas (2000-2008), da Firayim Minista kuma daga shekaraar Dubu Biyu da Takwas, zuwa Dubu Biyu da Goma Sha Biyu (2008-2012).

Ya sake zama shugaban ƙasa a shekarar Dubu Biyu da Goma Biyu (2012). Ya na da horo kwarai a kan Ilmin Shari’a (Lawyer).

Iyayensa su ne; Vladimir Spiridonovich Putin, wanda aka haife shi a shekarar Alif da Ɗari Tara da Goma Sha Ɗaya, zuwa Alif da Ɗari Tara (1911-1999), da mahaifiyarsa Maria Ivanovna Putina, ko kuma (Née Shelomova); Daga shekarar Alif da Ɗari Tara da Goma Sha Ɗaya, zuwa Alif da Ɗari Tara da Casa’in da Takwas (1911-1998).

Daga Alif da Ɗari Tar da Tamanin da Biyar, zuwa, Alif da Ɗari Tara da Casa’in (1985-1990), Putin ya yi aiki da KGB, Ƙungiyar Leƙen Asiri Ta Tarayyar Soviet.

Putin, ya yi aiki a Dresden, wanda wani ɓangare ne na tsohuwar Jamus ta Gabas, Bayan da Jamus ta Gabas ta ruguje a shekarar Alif da Ɗari Tara da Tamanin da Tara (1989), sai aka ce wa Putin ya dawo Tarayyar Soviet. Ya zaɓi zuwa Leningrad, wanda shi ne birnin da ya fi yawan Jama’a.

A watan Yunin, Alif da Ɗari Tara da Casa’in (1990), ya fara aiki a sashen Harkokin Ƙasashen Waje a Jami’ar Jihar Leningrad.

A watan Yunin, Alif da Ɗari Tara da Casa’in da Ɗaya (1991), an naɗa shi shugaban Kwamitin Ƙasa da Ƙasa na ofishin Magajin Garin Saint Petersburg. Aikinsa shi ne inganta alaƙar ƙasa da ƙasa da saka hannun jari na ƙasashen waje.

Putin, ya bar matsayinsa a cikin Ƙungiyar Leƙen Asiri Ta (KGB) a ranar Ashirin ga watan Agusta, na shekarar Alif da Ɗari Tara da Casa’in da Ɗaya (1991), a zamanin Shugaban Soviet Mikhail Gorbachev.

A cikin shekarar Alif da Ɗari Tara da Casa’in da Huɗu (1994), ya zama Mataimakin Shugaban Farko na birnin Saint Petersburg.

A watan Agusta, shekarar Alif da Ɗari Tara da Casa’in da Shida (1996), ya zo Moscow, kuma ya yi aiki a wurare daban-daban masu muhimmanci a cikin gwamnatin Boris Yeltsin.

Ya kasance shugaban FSB (sabon salo na KGB) daga Yulin, shekarar Alif da Ɗari Tara da Casa’in da Takwas, zuwa watan Agustan, Alif da Ɗari Tara da Casa’in da Tara (1998-1999), kuma ya kasance Sakataren Kwamitin Tsaro daga Maris zuwa Agusta, a shekarar Alif da Ɗari Tara da Casa’in da Tara (1999).

Putin Ya Zama Shugaban Rasha A Cikin Mayu 2000

Putin, shi ne shugaban jam’iyyar ‘United Russia’ mai mulki. Wannan jam’iyya ta kasance mai lashe zaɓukan Rasha tun bayan faɗuwar tarayyar Soviet.

Masu sukar Putin sun ce, ya ƙwace ƴancin mutane, kuma ya kasa sa ƙasar ta ci gaba. Rasha na samun kuɗi da yawa daga sayar da mai da gas zuwa wasu ƙananan kamfanoni, amma saboda cin hanci da rashawa, ba a amfani da kuɗin don inganta yanayin rayuwar jama’a.

Kwanan nan, ƴan adawar Rasha sun gudanar da tarukan adawa da gwamnati, sun yi kamfen ɗin nuna adawa da Putin a Intanet, kuma sun wallafa rahotanni masu zaman kansu ga jama’a baki ɗaya. Saboda takunkumi da aka sakawa kafafen watsa labarai, ya na da matuƙar wahala a fitar da bayanai daban-daban ga jama’a.

Putin, ya nuna adawa ga harin Ƙungiyar NATO a Libiya a shekarar Dubu Biyu da Ashirin da Ɗaya (2011). Ya na kuma yin adawa da da yaƙin Syria da takunkumi a kan ƙasar Iran, inda har ya sanya hannu wajen taimakawa Syria da ganin Gwamnatin Bashir Asad ba ta faɗi ba, da kuma taimakawa Iran ta ƙarƙashin ƙasa.

A tsarin mulkin Rasha, babu wanda zai iya zama shugaban ƙasa sau uku a jere. Saboda wannan, Putin bai gabatar da kansa ba don zaɓen Maris, na shekarar Dubu Biyu da Takwas (2008).

Ko ya ya, an ba ku damar zama shugaban ƙasa sau nawa kuke so, matuƙar ba zai wuce sau biyu a jere ba. A watan Maris, na shekarar Dubu Biyu da Goma Sha Biyu (2012), Putin ya gabatar da kansa don neman zaɓe, kuma ya samu kashi 64% na ƙuri’un da aka kaɗa. Wannan ya na nufin zai kasance shugaban Rasha har zuwa shekarar Dubu Biyu da Goma Sha Takwas ( 2018).

A ranar Shida ga watan Disambar, Dubu Biyu da Goma Sha Takwas (2017), Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa zai sake tsayawa takara a karo na huɗu a zaɓe mai zuwa, wato zaɓen Shugaban Ƙasar Rasha na shekarar Dubu Biyu da Goma Sha Takwas (2018).

A ranar Ashirin da Huɗu ga watan Maris, na shekarar Dubu Biyu da Goma Sha Huɗu (2014), an dakatar da Putin da Rasha daga ƙungiyar G8. Wannan ya faru ne saboda Amurka ta na tunanin cewa, rikicin Ukraine laifin Putin ne.

A watan Yulin shekarar Dubu Biyu da Ashirin (2020), masu jefa ƙuri’ar Rasha sun goyi bayan zaɓen raba gardama wanda zai ba Putin damar zama shugaban ƙasa har zuwa shekarar Dubu Biyu da Talatin da Shida (2036).

Vladimir Putin Kirista ne, memba ne na Cocin Orthodox ta Rasha.

A Ranar 28 ga Yuli, 1983 Vladimir Putin Ya Auri Lyudmila Aleksandrovna Ocheretnaya, Ta sadu da Vladimir Putin a Leningrad, kuma sun yi aure a ranar 28 ga Yuli 1983. Ma’auratan suna da ‘ya’ya mata biyu, Maria (an haife Ta a ranar 28 Afrilu 1985 a Leningrad, Tarayyar Soviet) da katerina (an haita shi a ranar 31 ga Agusta 1986 a Dresden, Jamus ta Gabas).

Yanzu dai, Putin gwauro ne, ya saki matar tasa.

A halin yanzu, shi ne gwauro mafi faɗa a ji a duniya.

 Game Da Arziki

A kan takarda, Shugaban Rasha Vladimir Putin ya zama kamar ɗan ƙasa mai tawali’u mai ƙarancin kuɗi. 

Fadar Kremlin ta yi iƙirarin cewa Putin na samun albashin shekara-shekara na dala 140,000. Kadarorinsa da ya bayyana a bainar jama’a sun hada da wani gida mai fadin murabba’in mita 800, tirela, da motoci uku. 

Sai dai a cewar wasu masana, mai yiwuwa shi ne wanda ya fi kowa kudi a duniya da kadarorin da suka kai dala biliyan 200.

Mamayewar Rasha a Ukraine a 2022

A ranar 24 ga Fabrairu, 2022, Rasha ta ƙaddamar da wani gagarumin farmaki a Ukraine, maƙwabciyarta ta kudu maso yammacin ƙasar, wanda hakan ke nuna ruruwar cigaban yaƙin dake gudana tsakanin Rasha da Ukraine tun daga shekara ta 2014. Sakamakon ƴanci da Ukraine ta samu na zama da kanta a shekarar 2014, wannan yaƙin an ayyana shi a matsayin mafi girman tashin hankali da ba’a taɓa gani ba a turai tun bayan yaƙin duniya Na Biyu, Akan kalli sanadin amatsayin Rasha tana son haramtawa Ukraine shiga ƙungiyar NATO bisa doka, ƙawancen ƙasashen Turai tare da Amurka da Kanada.

Kafin kai farmakin sai da Rasha ta amince da wasu jihohin Ukraine guda biyu da suka ayyana kansu amatsayin yan tattun ƙasashe, wato Jamhuriyar Jama’ar Donetsk da Jamhuriyar Jama’ar Luhansk, sannan kuma sojojin Rasha suka fara mamaye yankin Donbas na gabashin Ukraine a ranar 21 ga watan Fabrairu, 2022.

Da misalin ƙarfe 03:00 UTC (06:00 Moscow Time, MSK) a ranar 24 ga Fabrairu, shugaban Rasha Vladimir Putin ya bada sanarwar wani farmakin soji a gabashin Ukraine; mintuna kaɗan bayan haka, aka fara kai hare-haren manyan makamai a wurare daban-daban a cikin biranen ƙasar musamman ma wajajen jami’an tsaron ƙasar, ciki har da babban birnin kasar Kyiv da ke arewacin ƙasar. Hukumar kula da kan iyakokin Ukraine ta bayyana cewa an kai wa kan iyakokinta da Rasha da Belarus hari. Bayan sa’o’i biyu, sojojin kasa sun shiga da misalin karfe 05:00 UTC.[1] Ƙasashe da dama sun yi tir da harin tare da sanyawa Rasha takunkumi.

DAGA JARIDAR AMANA

Leave a Reply