Tashin farashin dala na daga cikin manyan matsalolin Najeriya – ƙwararru

0
43

Yayin da talakan Najeriya ke ci gaba da ɗanɗana kuɗarsa, hankula na daɗa karkata kan rawar da tashin farashin dala ke takawa.

Tashin farashin dala kan naira na daga cikin manyan dalilan ƙunci a tsakanin talakawan Najeriya, inda hakan ya ƙara ta’azzara bayan janye tallafin fetur.

Har yanzu mizanin tsallake talauci na Majalisar Ɗinkin Duniya na samun dala ɗaya a wuni bai canza ba, amma dala ɗaya ba za ta iya ƙosar da mutum ɗaya ba.

Shugabannin kasuwar canji da jami’an yaƙi da cin hanci, EFCC, ke zargi da haddasa tashin farashin dala sun nuna farin ciki da toshe kafar sadarwar yanar gizo ta BINANCE da ke jagorantar saye da sayar da kuɗin ƙetare.

Abubakar Abdullahi Dauran, shugaban kasuwar canji ta Abuja, ya ce “BINANCE da ‘yan Crypto ke tada farashin kuɗin, amma mu ko nawa dala ta kama mu na bin ‘yar riba ce kaɗan kuma mu ma tsadar farashin kaya ya shafe mu don kasuwa ɗaya mu ke ci da jama’a.”

Gwamnatin Najeriya ta ce ta na bin matakan samar da wadatacciyar dala ta hanyar masu zuba jari na ƙetare.
Muhammad Idris, ministan labaru na Najeriya, ya ce, “Ana maganar dala – dala to za mu jawo masu zuba jari daga ƙetare don wadatar da dalar a ƙasa kuma shugaba Tinubu ya samu nasarar yarjejeniyar shigo da jarin kimanin dala biliyan 30 da hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan yi.”

KU KUMA KARANTA:ECOWAS ta janye takunkumin da ta saka wa Nijar

Masanin tattalin arziƙi a Abuja Yushau Aliyu ya ce fa ce an koma aiki da Naira a cikin gida wajen hada-hadar kasuwanci da dillalan ƙetare ne da rage dogaro da shigo da kaya daga ƙetare za a iya cimma muradin dawo da darajar Naira.

Kamar yanda waɗanda a ke zargi da zama ‘yan barandan tada farashin dala ta yanar gizo, haka ma wasu ‘yan ƙasa ke yaɗa bayanan sauƙar dalar da zummar hakan ya yi tasiri kan farashin da ba shi da tabbas.

Leave a Reply