Siyasar Kano: Sabon rikici ya ɓarke tsakanin Kwankwaso da Ganduje

0
521

Daga Wakilinmu

Lokacin da Ganduje ya kai wa Kwankwaso ta'aziyyar rasuwar ƙaninsa a kwanan nan
Bayanan hoto,Lokacin da Ganduje ya kai wa Kwankwaso ziyarar ta’aziyyar rasuwar ƙaninsa a kwanan nan

A daidai lokacin da ake ta raɗe-raɗin yin sulhu tsakanin tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da magajinsa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, wani sabon rikicin siyasa ya sake kunno kai tsakaninsu.

Yayin wata hira da jaridar Punch a ranar Asabar, Kwankwaso ya bayyana nasarar da Ganduje ya samu a zaɓen 2019 a matsayin haramtacciya, yana cewa wasu gaggan ƴan siyasa ne daga sama suka ƙaƙaba wa al’ummar jihar Kano shi.

“Sun tursasa wa ɗumbin mutane ra’ayin wasu ƴan tsiraru wanda hakan shi ne laifi mafi muni a tsarin dimokuradiyya. Ina tsammanin sun fahimci kuskurensu a yanzu, wasunsu na ƙoƙarin gyara kura-kuransu a yanzu bayan barnar da aka yi wa jihar Kano. Abin takaici ne yadda suka kasa ganin abin da talakawa suka hango wa kansu.”

Ya ci gaba da cewa ”Muna da ƙarfin da za mu iya hana su abun da suka so yi a wannan lokaci, amma muka buƙaci matasanmu su kwantar da hankalinsu, muka bar su da aniyarsu, muka bi matakin shari’a, amma a nan ma aka yi abun da aka yi” in ji Kwankwaso.

Sai dai wata sanarwa da ta fito daga fadar gwamnatin jihar Kano mai ɗauke da sa hannun Kwamishinan Watsa Labaran jihar Muhammadu Garba, ta bayyana kalaman na Kwankwaso a matsayin shaci-faɗi da ko kaɗan babu ƙanshin gaskiya a cikinsu.

”Abun takaici ne yadda a matsayin Kwankwaso na shugaba, wanda ake damawa da shi a harkokin gudanar da zaɓe ya kasa amincewa da sakamakon zaɓen da hukuma mai zaman kanta ta gudanar kuma kotu ta amince da shi” in ji sanarwar.

Gwamnatin ta Kano ta ci gaba da cewa hirar da Kwankwason ya yi da jaridar Punch ta janyo masa mummunar illa ne fiye da alfanun da ya yi tsammanin za ta haifar masa.

A cewarta a fili take cewa Kwankwaso ya fahimci gwamnatin Ganduje ta tsere wa sa’a wajen shimfiɗa muhimman ayyuka ga jama’a, shi ya sa yake ganin ana ƙoƙarin shafe abun da yake ganin ya yi a nasa

”Kwanan nan aka ji shi ya jan hankalin magoya bayansa su kaucewa furta miyagun kalamai amma sai ga shi ya ɓige da yi shi da kansa, ko kaɗan wannan bai dace da shi ba”, a cewar sanarwar

Leave a Reply