Jami’an Duba-gari Za Su Fara Aiki Gida-gida A Jihar Kaduna – Maimunatu

0
348


Mustapha Imrana Abdullahi
Janar Manajar hukumar kiyaye muhalli ta Jihar Kaduna Maimunatu Abubakar, ta bayyana cewa jami’an hukumar za su fara gudanar da aikin duba muhalli a duk fadin Jihar Kaduna a cikin watan Janairu 2022 domin tabbatar da al’amuran lafiya da na muhalli sun ci gaba da inganta.
Maimunatu Abubakar ta bayyana hakan ne lokacin da take ganawa da manema labarai a ofishinsa da ke hukumar KEPA cikin garin Kadina.
Maimunatu Abubakar ta ci gaba da cewa tuni shirye shirye sun yi nisa wajen ganin jami’an sun shiga Gida Gida,kwararo kwararo wato layi layi domin tabbatar da tsafatar muhalli.
“Zamu shiga ko’ina da ina saboda haka kamar yadda doka ta ba mu ikon gudanar da aiki idan muka ga mutane sun kasa gyara kwatar da suke amfani da ita ko wata kazantar da bai kamata a gani a inda mutane ke zama ba hakika zamu hukunta mutum ko waye, domin muna da kotun tafi da gidanka wadda za ta zartarwa da mutum hukunci nan take”, Inji Janar Manaja Maimunatu Abubakar.
Ta kuma kara da bayanin cewa hukumar zata tabbatar da jami’anta sun bi Gida Gida sun dauki sharar da mutum yake da ita kuma kowa aka daukewa sharar da ya tara zai biya kamar yadda tsarin Jihar ya tanadar.
“Ta yaya wani zai kwashe maka datti ko kazantar da ka tara a cikin Gidanka ai ya dace kowa ya kwashe duk wani dattin da kazantar da mutum ya tara da kansa, saboda haka a wannan watan daya na Janairu za a fara aiwatar da wannan aiki gida gida kwararo kwararo ta yadda za a samu ingantaccen tsarin tsaftace muhalli a ko’ina”.
Ta kara da cewa ya dace jama’ar Jihar Kaduna su ci gaba da yin godiya ga Allah madaukakin Sarki da ya ba su Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i a matsayin Gwamna, saboda suk irin tsarin da ake gani a garin Abuja na tsari da kuma tsafta a ko’ina da ina cikin Abuja duk aikin Malam Nasiru ne lokacin da yake matsayin ministan Abuja”.
“A lokacin ina aiki a Abuja ya dauke mu sai da muka je birnin Fatakwal a kalaba  domin samun irin tarihi da kuma yadda tsarin tsaftar muhalli ta Gari da dukkan muhalli take wanda hakan aka yi a birnin Abuja wanda a yanzu kwalliya ke biyan kudin sabulu, har kowa ke sha’awar birnin Abuja a yanzu”.
Janar Manaja ta hukumar KEPA da ke aikin kiyaye muhalli, Maimunatu Abubakar ta ci gaba da yin kira ga jama’a da su bayar da hadin kai da goyon baya ga wannan aikin inganta muhalli da lafiyar jama’a da suke kokarin farawa a halin yanzu,kasancewar aiki ne da zai taimakawa kowa ya fuskar inganta lafiyar muhalli da kuma ta jikin bil’Adama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here