Shugaban Karamar Hukumar Bichi Ya Mika Gaisuwar Sallah Ga Al’ummar Yankin

0
279

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

SHUGABAN majalisar karamar hukumar Bichi, Dokta Yusuf Mohammed Sabo, ya mika sakon sa na Gaisuwar Sallah ga daukacin al’ummar yankin tare da fatan Allah ya maimaita mana bisa kwanciyar hankali da kuma karuwar arziki.

Dokta Sabo, ya kuma yi fatan cewa za a ci gaba da gudanar da zamantakewa bisa yadda aka koyi darussa cikin watan Ramadan musamman wajen kyautata mu’amulla da kuma gudanar da ibada mai albarka ta yadda za a ci gaba da amfanar aiyukan alherin da aka yi lokacin azumi.

Sannan ya taya gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da mai martaba sarkin Bichi Alhaji Nasir Ado Bayero da daukacin hakiman masarautar Bichi da kuma majalisar karamar hukumar ta Bichi murnar kammala ibada lafiya.

A karshe, Dokta Yusuf Mohammed Sabo, ya kara jaddada cewa zasu ci gaba da aiwatar da kyawawan manufofin gwamnatin sa ta yadda al’ummar wannan yanki zasu amfani ribar dimokuradiyya a kowane lungu da sako na fadin Karamar hukumar ba tare da nuna gajiyawa ba.

Leave a Reply