An Bukaci Al’ummar Musulmi Da Su Yi Aiki Da Darussan Ramadan

3
310


JABIRU A HASSAN, Daga Kano.


SHUGABAN Karamar hukumar Dawakin Tofa Alhaji Ado Tambai Kwa ya yi Kira ga al’ummar musulmi da su ci gaba da yin aiki da darussan da suka koya cikin watan Ramadan musamman wajen sada zumunci da kaunar juna.


Ya yi wannan tsokaci ne yayin ganawar su da wakilin mu, inda kuma ya kara da cewa watan Ramadan wata ne dake koyar da darussa masu tarin yawa wadanda suka hada da kaunar juna da zumunci da Kuma taimakon al’umma kamar yadda aka yi cikin wannan wata.


Alhaji Ado Tambai ya kuma bayyana cewa yana dakyau al’ummar musulmi a duk inda suke, su rika yin waiwaye dangane da abubuwan da suka wakana na alheri da ibada tukuru domin ci gaba da rabauta daga ribar aiyukan da suka gudanar da kuma abubuwan da za suyi bayan kammala ibadar Azumi.


Shugaban Karamar hukumar ta Dawakin Tofa ya kuma mika sakon sa na barka da Sallah ga gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da al’umar karamar hukumar ta Dawakin Tofa da jihar Kano da kasa baki daya dama daukacin al’umar musulmin duniya tareda fatan Allah ya maimaita mana ya Kuma ci gaba da baiwa kasarnan zaman lafiya da karuwar arziki.

3 COMMENTS

Leave a Reply