Sabon Mai Bayar Da Shawara Kan Harkokin Shari’a Ga APC Ya Karbi Takarda

0
368

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

SABON mai bayar da shawara a kan harkokin shari’a na Jam’iyyar APC a matakin kasa Barista Ahmes El- Marzuk, ya karbi satifiket na tabbatar da zabensa da aka yi.

El-Marzul, ya dai karbi wannan sabon satifiket ne daga sabon shugaban Jam’iyyar APC na kasa Alhaji Sanata Abdullahi Adamu a ranar Laraba a hedikwatar Jam’iyyar ta kasa da ke Abuja a tarayyar Najeriya.

Shi dai Barista Ahmed El- Marzuk, ya yi karatun zama Lauya ne a Jami’ar Bayero da ke Kano.

Leave a Reply