Rikicin Manoma Da Makiyaya: Kungiyar AFAN Da Miyetti Allah Zasu Samar Da Zaman Lafiya

0
324

JABIRU A HASSAN, Daga Dutse.

KUNGIYOYIN manoma da makiyaya na Jihar Jigawa za su yi aiki tare domin magance yawaitar rikice-rikice da ake yi tsakanin manoma da makiyaya a Jihar, tare da jaddada hada hannu da gwamnatin Jihar ta Jigawa domin cimma nasarar wannan aiki.

Shugabannin kungiyar sune suka bayyana haka a tattaunawar su da wakilin mu a birnin Dutse, inda kuma suka nunar da cewa abubuwan da suka faru a makon da ya gabata a Jihar bai yiwa kowane bangare dadi ba.

Alhaji Idris Yau Mai Unguwa, shugaban kungiyar manoma ta kasa reshen Jihar Jigawa wato (AFAN), ya bayyana cewa ko shakka babu rikicin da ya faru a yankin Guri tsakanin manoma da makiyaya bai yiwa kungiyar ta AFAN dadi ba, don haka zasu kara hada karfi da makiyaya domin daukar matakai na kawar da aukuwar fadace-fadace tsakanin bangarorin biyu.

Haka kuma ya sanar da cewa zasu ci gaba da kokari wajen ganin an kawo karshen rikici tsakanin manoma da makiyaya a Jihar ta Jigawa ta yadda za a ci gaba da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali duba da yadda kowane bangare yake da muhimmanci ga zamantakewar dan Adam”.

Mai Unguwar, ya yi amfani da wannan dama wajen yin Kira ga daukacin manoman Jihar Jigawa da su ci gaba da kasancewa masu bin doka da kaunar zaman lafiya kamar yadda aka san su, tare da jinjinawa gwamnatin Jihar Jigawa bisa jagorancin gwamna Muhammad Badaru Abubakar saboda kokarin da gwamnatin sa keyi wajen inganta zaman lafiya a fadin Jihar.

A nasa bangaren, shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah Alhaji Adamu Idris Babura, Kira ya yi ga makiyaya da su kara hakuri da nuna juriya wajen ganin an sami maslaha a duk lokacin da wata matsala ta faru, sannan ya jaddada cewa suna daukar Muhimman matakai na warware duk wata rashin jituwa da makiyaya suke ciki tsakanin su da manoma.

Haka kuma shugabannin sun yi amfani da wannan dama wajen yin ta’aziyya ga iyalai na wadanda suka rasa rayukansu yayin rikicin, tare da fatan samun sauki ga wadanda suka sami raunuka sanadiyyar wannan rigima ta makiyaya da manoma.

Idan dai za a iya tunawa, an sami rikici tsakanin manoma da makiyaya a yankin Guri inda aka kashe mutane 3 da jikkata wasu mutane 15 wanda ya zuwa yanzu kungiyoyin guda biyu suka himmatu wajen ganin an sami kwanciyar hankali da maslaha dangane da abubuwan da suka faru.

Leave a Reply