Ramadan Iftar: Burina Shi Ne Naga An Karfafawa Mata – Maryam Mai Rusau

0
403

Daga; Abdullahi Alhassan, Kaduna.

SHUGABAN Mata a Jami’yyar APC ta Jihar Kaduna Hajiya Maryam Sulaiman wacce akafi sani da Mai Rusau, ta ce burin ta shi ne taga an Karfafawa Mata, Kasan cewar su Iyayen al’umma ne kuma bugu da kari masu taka muhimmiyar rawa wurin kafa Gwamnati a ko wani mataki a kasar nan.

Hajiya Maryam Mai Rusau, ta bayyana haka ne jim kaɗan bayan ta gama bude baki da Kungiyoyin Mata a Sakatariyar jam’iyar APC dake Kaduna, inda ta kara da cewar ta kira wannan taron ne don ganawa da Mata Kasancewar su masu taka muhimmiyar rawa wajen ganin an cimma nasarar a kan kowani al’amari.

Mai Rusau, ta kara da cewar “mun wayar masu da kai kan mahimmanci karbar katin zabe kasancewar zabe na kara karantawa, haka kuma mun karbi korafe- korafen su, kan yadda tafiyar aka yi ta a baya, inda muka yi alkawarin aiwatar da abinda zai kawo ci gaba a wannan karon.

Hajiya Maryam Mai Rusau, ta kuma bayyana irin Shirye Shiryen da Jam’iyar APC take dashi kan tallafawa Mata da Sana’o’i don su zama masu dogaro da kansu tare kuma da basu Jari don ganin sun habbaka Sana’o’in da suka koya.

Daga karshe, ta yi kira ga yan Siyasa dama Masu hannun da shuni kan tallafawa Mata, musamman ma wadanda suka rasa mazajensu, ta hanyar daukar nauyin koyar dasu Sana’o’in daban-daban.

Ita kuwa a nata jawabin, Shugaban Mata ta jam’iyyar APC shiyya ta biyu, Hajiya A’isha Idris, yabawa kokarin Shugaban Matar ta yi na ganin cewa an Karfafawa Matan kasancewarsu jigo a tafiyar da jam’iyyar tare kuma da fatan ci gaba da karfafawa matan kwarin gwiwa ta hanyar koyar dasu Sana’o’in da zasu dogara da kan su.

Su kuwa mahalarta taron bude bakin da shugabar Matan ta shirya, yabawa shugabar Mata ta jam’iyyar APC su ka yi na ganin ta haɗa kansu tare kuma da jin korafe- korafen su don ganin an sauya salon gudanar da Jam’iyyar a Jihar Kaduna.

Taron dai ya samu halartar Kungiyoyin Mata daga Shiyyoyi uku da ake dashi na Siyasa a Jihar Kaduna.

Leave a Reply