Bola Tinubu Ne Dan Siyasar Da Ya Yi Karkon Da Tauraruwarsa Ke Haskawa – Dan Jarida Ali

0
377

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

AN bayyana shahararren dan siyasar tarayyar Najeriya Bola Ahmad Tinubu a matsayin mutumin da ya fi duk wani dan siyasa karko tun bayan da ya sauka daga matsayin Gwamnan Jihar Legas, amma tauraruwarsa ke kara haske a koda yaushe.

Dan Jarida, Ali M Ali ne ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da kafar Talbijin ta Kaftan Hausa da ke da babban ofishinsu a Abuja.

Ali M Ali, ya ce idan za a yi duba na musamman kuma a tsanake, za a iya gane cewa babu wani dan siyasar da ya yi karko tun da ya sauka daga Gwamnan Jihar Legas ” babu abin da Bola Tinubu ke yi sai kafa mutane a matakai daban daban wanda hakan ya Sanya ya zama mutumin da ke da ruwa da tsaki a kusan ko’ina a fagen siyasa da matakin Gwamnatin tarayya”.

Ya kara da cewa sakamakon kokari da kwazon aiki na dan siyasa Bola Ahmad Tinubu ya sa a lokacin da yake Gwamnan Jihar Legas tattalin arzikin Jihar ya inganta har ta kai Jihar ta tsaya da kafafunta har kananan hukumomi suka samu damar zama da kansu a lokacin mulkin Obasanjo.

“A lokacin da Bola Tinubu na Gwamnan Jihar Legas ya kirkiri kananan hukumomi sai shugaban Najeriya na wancan lokaci Obasanjo ya hana aba kananan hukumomin Legas kudi amma sakamakon kokari da jajircewa, Bola Tinubu duk ya ci gaba da rike kananan hukumomin, kuma sai da tattalin arzikin Jihar Legas ya kasance tamkar tattalin arzikin wasu kasashen Afrika da yawa da a kididdiga ake bayanin cewa ya kai na kasashe a kalla biyar duk kuma sakamakon jajircewarsa ne da kwarewar aiki”.

Kuma wani babban abin duba wa a halin yanzu shi ne tauraruwar Bola Tinubu ce ke haskawa a fagen siyasar Najeriya don haka ake ganin ya na da damar dare shugabancin mulkin kasar nan.

Leave a Reply