Ban Fita Daga Jam’iyyar APC Ba – Sanata Kabiru Marafa

0
484

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

TSOHON Sanata Kabiru Garba Marafa daga Jihar Zamfara ya bayyana cewa har yanzu ba su fice daga cikin jam’iyyar APC ba.

Tsohon Sanatan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da kafar yada labarai ta Tambarin hausa.

Kabiru Garba Marafa ya bayyana cewa a iya saninsa akwai jam’iyyu da yawa da suka nemi tattaunawa da su sakamakon irin yadda tsofaffin shugabannin APC na kasa suka yi masu kuma har yanzu su na tattaunawa da su.

Amma batun ficewa daga APC shi bai san wannan ba kuma kowa ya bayar da sanarwar hakan kuskure ya yi domin kamar yadda suke tattaunawa da sauran wasu jam’iyyu haka PDP ma ta nemi su tattauna kuma har yau ba a kammala tattaunawar ba.

Don haka ba gaskiya ba ne cewa mun koma PDP sam ba a yi wannan ba, ana dai tattaunawa da jam’iyyu kuma sun ce za su yi mana abin da aka kasa yi mana a APC.

Leave a Reply